Yadda ’yan bindigar Katsina su ka kama ‘yan makarantan Islamiyya 80, a wajen tattakin Maulidi

0

Wasu ’yan bindiga sun tare daliban Islamiyya su talatin su ka tasa keyar su cikin daji, a Karamar Hukumar Dandume cikin Jihar Katsina.

Lamarin ya faru a ranar da aka damka daliban Kankara su 344 a hannun iyayen su, bayan an kubutar da su daga hannun ’yan bindiga.

An kama yaran wadanda yawancin su ‘yan mata ne da su ke kan hanyar komawa gida Mahuta, daga halartar taron maulidin Annabi (SAW) da dare.

An kama yaran wadanda ‘yan makarantar Islamiyya ne, misalin karfe 11:20 na dare, lokacin da su ke kan hanyar komawa gida daga halartar majalisin Maulidi.

Mazauna garin sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa bayan kama yaran sai ‘yan bijilante da jami’an tsaro su ka darkaki ‘yan bindigar, har aka samu nasarar kubutar da su.

Sai dai har yanzu ba a sani ba ko sun gudu da wasu daga cikin wadanda su ka kama din.

Amma di jami’an ‘yan sanda sun ce an kubutar da yaran baki dayan su.

Jami’an ‘yan sandan Katsina sun ce an ceto yaran baki daya, tare da kubutar da wasu shanu guda 12 daga hannun maharan.

Gambo Isa, Kakakin Yada Labarai na Rundunar ’Yan Sandan Katsina, ya shaida wa manema labarai cewa yaran ‘yan Mizburrahim Islamiyya ce da ke garin Mahuta, kuma su 80 ne.

Ya ce sun je taron Maulidi ne a kauyen Unguwar Alkasim da ke Karamar Hukumar Dandume.

Mahara sun tare su ne, bayan sun fito daga fashi, inda su ka kamo mutum hudu da shanu 12 a kauyen Danbaure cikin Karamar Hukumar Funtua, daga nan ne suka cimma ‘yan maulidin a daidai suna salatuttika, zikiri.

Share.

game da Author