Yadda muka ceto daliban Kankara –Sojoji

0

Rundunar Sojojin Najeriya ta yi ikirarin cewa sojojin ta ne su ka ceto daiban Kankara su 344, wadanda aka yi garkuwa da su tsawon kwanaki shida.

Yanzu dai an samu baki hudu kenan na bangarorin da suka yi ikirarin karbo yaran.

Yayin da Gwamna Matawalle na Zamfara ya furta wa BBC Hausa cewa shi ne ya nemi taimakon Shugaban Miyetti Allah na Kasa ya shiga tsakani, shi ma Gwamna Aminu Masari ya yi ikirarin karbo yaran, ba tare da ya ambaci sa hannun Gwamna Matawalle ba.

Ranar Asabar kuma sojojin Najeriya sun ce su ne su ka shiga jeji su ka ceto yaran daga hannun ’yan bindigar da su ka sace su tun a ranar 11 Ga Disamba.

Sojojin sun ce duk da cewa an yi ta sa-toka-sa-katsi wajen sasantawa su saki yaran ta wasu bangarorin shiga tsakani, maharan sun nemi jan tunga tare da kokarin kin sakin yaran, har su ka yi wa sojoji kwanton-bauna.

Babban Kodinatan Yada Labarai na Hedikwatar Tsaro, John Enenche da Ahmed Jibrin, tsohon Daraktan Leken Asiri na Sojojin Najeriya, sun bayyana yadda lamarin ceto yaran ya faru, a cikin wani shiri na musamman a Gidan Talbijin Na Kasa.

Jibrin da a yanzu shi ne Mashawarci na Musamman kan Harkokin Tsaro ga Ministan Tsaro, Bashir Magashi.

Jibrin ya ce bayan an kama yaran, Minista ya tura tawaga zuwa Kankara da Katsina wadda ta kunshi Hafsoshin Najeriya da Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro.

Ya ce Minista ya bada odar cewa lallai a bi ka’idoji da matakan da ya kamata a bi, ta yadda ba za a bude wuta har a rasa ran yaro ko daya ba.

“Bada wannan umarni ke da wuya zaratan sojoji su ka tabbatar sun kewaye dajin, ta yadda babu hanyar da maharann za su iya kubuta.

“Maharan duk sun sani cewa an kewaye su ko ta ina, kuma ta sama ma su na ganin jirage na shawagi, ba su hanyar kubuta kenan.

“Lokacin da sojoji su ka matsa kusa da inda aka tsare yaran, wasu tsageru sun dan yi masu tirjiya, amma aka kakkabe su aka yi gaba, aka kara nausawa a cikin surkukin jejin.

Ya ce ba a dai rasa ran yaro ko daya ba, amma an kashe wasu mahara wadanda su ka nemi yi wa sojoji tsaurin-ido, ta hanyar kokarin hana su kara nausawa a cikin dajin.

Ya ce lokacin da sojojin ke kakkabe burbushin wadanda su ka nemi tare masu hanya, a gefe daya kuma ana can ana tattauna yadda za a saki yaran.

Sai dai kuma ya ce sojoji ba su bude wuta ga wadanda ke rike da yaran ba, don gudun kada a yi asarar rayukan yaran.

Ya ce duk zancen wofi ne da cika-baki Shekau ke yi da ya ce Boko Haram ne su ka kama yaran.

Share.

game da Author