Jagoran jam’iyyar APC Bola Tinubu ya bayyana cewa ceto ‘yan makarantan Kankara da jami’an tsaro suka yi nuni ne cewa lallai Buhari a tsaye yake wajen ganin an kawo karshen ta’addanci a kasar nan.
Tinubu ya kara da cewa jajircewa da gwamnan Katsina Aminu Masari yayi abin yabawa ne, da kuma kwazon da dakarun tsaron kasa suka yi har Allah ya sa aka yi nasara fin karfin maharan aka ceto yaran daga hannun su.
A karshe ya ce duk da samun nasara da aka yi, ya hori jami’an tsaro da su kara zamma a wajen yaki da ta’addanci da suke yi a yanzu domin kawo karshen sa kwata-kwata a kasar nan.
Idan ba a manta ba a rabar Alhamis ne aka ceto yaran makarantan sakandaren Kankara daga hannu ‘yan bindiga bayan sun dauki kwanaki 6 ysare hannun su.
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce gwamnati bata biya ko sisi ba a wajen tattauna sako’ yan makarantan.
Shima shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yabawa gwamna Masari da jami’an tsaron Najeriya kan ganin an yi nasaran ceto yaran.
A jawabi da yayi musu a dakin taro na gidan gwamnati, Buhari ya hori yaran da su manta da abinda ya faru da su, su maida hankali a karatun su.