NDLEA ta damke wasu matafiya biyu da hodar ibilis mai nauyin kilogiram 14.4 a filin jirgin saman Abuja

0

Hukumar (NDLEA), ta damke wasu matafiya biyu a filin jirgin saman Abuja dauke da hodar ibilis mai nauyin kilogiram 14.4.

Kakakin hukumar NDLEA Jonah Achema ya sanar da haka a wani takarda da ya fitar ranar Alhamis.

Achema ya ce sun kama wannan hoda mai yawa ne daga jakukkunan wasu matafiya biyu a Abuja.

Ya ce an kama hodar ibilis mai nau’yin kilogiram 7.2 daga wani dan kasar Brazil da kuma mai nauyi irin haka a jakan wani dan Najeriya wanda shima daga kasar Brazil din yake tafe.

Shi dan kasar Brazil din mai suna Mailson Mario mai shekaru 23 ya loda kwalin cakulet makil da hodar shi kuma dan Najeriya Elechi Adendu Kingsley mai shekaru 39 da ya yi tsawon shekara 13 a kasar Brazil ya saka tasa hodar ce a cikin jaka.

Share.

game da Author