Korona ta kashe Janar din da ya yi sanadiyyar tashi taron Buratai na shekara-shekara

0

Wata majiya daga sojojin Najeriya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES rasuwar Manjo Janar Olu Irefin, sojan da aka tabbatar ya kamu da cutar korona, ya fadi kasa a wurin Taron Shekara-shekara na Manyan Hafsoshi da Janar Buratai ya shirya.

Bayan Irefin ya fadi a wurin taron a ranar Talata, an garzaya da shi asibiti, inda aka gano cewa cutar korona ce ta kama shi.

Wannan ya haifar da bada sanarwar tashi daga taron na shekara ta 2020, tun kafin ranar kammala taron.

Manjo Janar Irefin dai shi ne Babban Kwamandan Bataliya ta 6 ta Sojojin Najeriya da ke Fatakwal, Jihar Ribas.

Kafin nada shi kwamadan Fatakwal, Irefin shi ne Kwamandan Bataliya ta 81 da ke Lagos.

Wakilin PREMIUM TIMES ya buga wa Kakakin Sojojin Najeriya, Sagir Musa waya, domin jin ta bakin sa, amma bai amsa ba.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda korona ta fasa taron da Janar Buratai ya shirya, ta hargitsa shirye-shiryen bikin dan sa Hamisu. Amma a lokacin ba ta bada bayanin suna da mukamin sojan da ya kamu da cutar ba.

Tsakanin ranar Talata da Laraba dai sama da mutum 1,000 ne su ka kamu da cutar korona a Najeriya.

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Buratai ya soke sauran shirye-shiryen da su ka rage na Taron Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya da ya shirya.

An tashi daga taron babu shiri, saboda an samu mai cutar korona a cikin mahalarta taron.

Kakakin Sojojin Najeriya Sagir Musa ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Alhamis.

Sagir ya ce a n samu mai dauke da cutar a ranar Talata.

Sanarwar ta umarci duk wani wanda ya san ya halarci taron da ya gaggauta killace kan sa, kamar yadda dokar da gwamnatin tarayya ta gindaya.

Haka nan kuma Janar Buratai ya sanar cewa an hana duk wani da ya halarci taron halartar zuwa saurin auren dan sa Hamisu Buratai, wanda za a yi a ranar Juma’a.

Buratai ya yi wa kowa fatan alheri, amma ya ce duk wanda ya je taron, to an dauke masa nauyin halartar daurin auren dan sa.

Share.

game da Author