Matar soja ta yi yaji, ta tare a gidan saurayi

0

Wani sojan sama da ya yi ritaya mai suna Richard Imana ya shigar da kara a wata kotu dake Iyana-Ipaja jihar Legas yana tuhumar matarsa da yi masa yaji amma kuma tarewa tayi a gidan saurayi.

Imana ya ce baya ga kama gabanta da tayi, ta ta fi masa karamin dan su daya.

” Nkem ta tare a gidan saurayinta a lokacin da nake Barno muna can muna gwambzawa da Boko Haram. Ko da na dawo sai na yi ritaya daga aikin sojan ma kawai domin in kula da ‘ya’yan mu uku.

Imana ya ce shi fa haryanzu yana son matarsa, abinda yake so ta dawo gida su ci gaba da zama sannan ta dawo masa da dansa.

Matar tasa Nkem mai shekaru 34 ta karyata zargin Imana cewa wai ta koma da zama gidan saurayinta ne. Ta ce gidan makwabciyan ta ta tafi ta ke zama da ita kuma a barikin da suke ne. Sannan kuma dan nasu ta tura shi wajen kakar sa ne domin ta taya ta rike shi na dan wani lokaci.

” Tunda Imana ya koma Barno da aiki, ya daina turo min kudin abinci kwata-kwata. Na gaji ne kawai shine ya sa na yi yaji.

Ita ma Nkem ta bayyana wa kotu cewa tana son mijinta. ” Ina rokon kotu ta sasanta tsakanin mu ne ne mu koma mu yi zaman soyayya kamar ada.

A Karshe Alkalin kotun Adewale Adegoke dora wa Nkem laifi ne bisa ficewa da tayi daga gidanta koma wani gidan can tana zamam sannan ta waske masa da da daya.Ya hore su da su zauna lafiya da juna.

Za a ci gaba da shari’a ranar 15 ga watan Disamba.

Share.

game da Author