Majalisar ta Tarayya ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta dakatar da Shirin Daukar Ma’aikata 774,000, sannan kuma ya maida Shugaban Hukumar Samar Da Aiki (NDE), Nasir Argungu.
Majalisar Tarayya ta ce Buhari ya cire Argungu saboda an ba shi gurguwar shawara, alhali Argungu ba shi da wani laifi, sai kawai don ya tsaya tsayin-daka cewa a bi gaskiya da ka’ida, wajen daukar ma’aikata 774,000 da za a fara daga kananan hukumomi 774 na kasar nan.
Hon Olajide Olatunbosun ne ya fara tayar da wannan magana, kuma nan take aka rika goyon bayan sa daya-bayan daya a zaman da Majalisa ta yi na ranar Talata.
Sun ce akwai kwamacala da ruguguwa a cikin shirin, don haka a dakatar da shi.
Sun ce Nasiru Argungu da Shugaba Muhammadu Buhari ya cire a ranar 7 Ga Disamba, ba shi da wani laifi, Buhari ya cire shi ne bisa wata gurguwar shawara da aka ba shi kan rudanin da ke tartare da shirin daukar ma’aikata 774,000.
Kan haka su ka shawarci Buhari ya dakatar da shirin. Sun ce tunda an maida shirin sai cikin 2021 za a fara, don haka Buhari ya tsaida shirin har sai an samar masa wuri a Kasafin 2021 tukunna.
Wannan shiri dai ya haifar da rikici tsakanin ‘yan majalisa da Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo.
Keyamo ya zargi ‘yan Majalisa da kokarin handame wadanda za a dauka ayyukan, duk kuwa da cewa an ba su alfarmar kawo kashi 15 bisa 100 na yawan ma’aikatan da za a dauka din.
Ana ganin cewa Keyamo ne ya shawarci Buhari ya cire Shugaban NDE, Nasiru Argungu, saboda zargin ya na goyon bayan matsayar da ‘yan Majalisar Tarayya su dauka a rikicin su da Minista Keyamo.
Yanzu dai Majalisar Tarayya ta kuma umarci Ministar Harkokin Kudade kada ta saki kudi naira bilyan 52 da aka yi niyyar amfani da su wajen gudanar da ayyukan.
Sun ce a tsaya har a warware tankiya, har a maida Argungu kan aikin sa, kuma har sai an shigar da shirin cikin kasafin 2021 tukunna.