An nada Sanusi Sarkin Kano don a watsa wa Jonathan kasa a ido ne, shi ya sa na wancakalar da shi – Ganduje

0

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa da gangar aka nada Sanusi Lamido Sarkin Kano a lokacin yana mataimakin gwamnan jihar domin a ci wa Jonathan Mutunci.

Ganduje ya fadi haka a jawabin sa wajen kaddamar da wata sabuwar littafi da aka rubuta kan tsohon shugaban Kasa, Goodluck Jonathan.

” Bari in gaya muku, ko a lokacin da aka nada Sanusi sarkin Kano, an nada shi ne don a ci wa Jonathan mutunci. A nuna masa bai isa, ko yana so ko baya so sai an nada shi. Amma ni na san cewa bai cancanta ba.

” Abinda ya sa aka nada shi sarkin Kano, shine wai domin a nuna ma Jonathan mutanen Kano na son sa duk da ya yayi maganin sa, wato tsigeshi da yayi a lokacin da ya tona harkallar bacewar wasu kudaden NNPC har dala biliyan 20 daga kujeran gwamnan Babban Bankin Najeriya.

Ganduje yace yayi likimo ne yana jiran ya samu dama don yayi maganin Sanusi, ” Irin wannan magani da Jonathan ya ba Sanusi wato tsigeshi daga kujerar gwamnan babban bankin Najeriya, ni ma sai na dauko kwaya daya cikin maganin na bashi. Ya tattara kayan sa ya fice daga gidan sarautar Kano.

” Duk da cewa ni ba likita bane, amma dai wannan kwayar magani da Jonathan ya samo a wannan lokaci yayi min aiki domin mara lafiyan dai da ya dirka wa maganin a wancan lokaci, shine ya ke bukata a yanzu a sake dirka masa ya kama gaban sa, tuni kuwa na dirka masa gari ta samu lafiya.

Share.

game da Author