Kungiyar Jinkai ta Duniya (Amnesty International), ta bayyana cewa matsalar tsaron da Arewa ke ciki ta jefa harkar ilmi a yankin cikin gagarimar barazana.
Kungiyar ta ce kama dalibai 333 a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Kankara a Jihar Katsina, barazana ce kai-tsaye ga ilmin zamani a Arewa.
” Dangane da abin da ke faruwa a Arewa, ya zama wajibi a samar da tsaro ga dukkan makarantu. Kada a bar dalibai wasarere cikin yanayin da zai samu kan sa a zabi daya cikin biyu, wato ko ilmi ko ran sa.”
Haka Daraktan ‘Amnesty International’ a Najeriya, Osai Ojigho ya bayyana.
Ranar Talata wani bidiyo ya nuna Shekau na cewa su su ka sace daliban.
” Mu ne muka kama su domin mu daukaka addinin Musulunci. Mun yi haka ne domin mu hana yara karantun boko. Saboda Allah da Annabin Allah ba su halasta wa musulmi yin karatun boko ba.” Inji Shekau, cikin bidiyon da HumAngle ta yi ikirarin gani.
‘Amnesty International’ ta cewa kashe-kashe da hare-haren da ake yi a Arewa ta jefa kananan yara cikin bala’o’i.
Ta ce ana kama kananan yara ana tilasta su shiga ta’addanci, ta hanyar sa su daukar makamai.
” Wannan abu ya yi kamari, domin ga shi nan daliban Katsina ma sun fada hannun ‘yan ta’adda, masu maida kananan yara sojojin dole.
Amnesty international ta yi kiran da a gaggauta ceto yaran.
Kungiyar ta kuma nuna takaicin cewa an kashe daruruwan malaman makaranta daga farkon yakin Boko Haram zuwa yanzu.