Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 318 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –104, Kaduna -59, FCT-50, Rivers-17, Ogun-16, Kano-14, Nasarawa-14, Akwa Ibom-10, Katsina-10, Edo-7, Oyo-5, Sokoto-5, Filato-4 da Taraba-3
Yanzu mutum 69,255 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 64,774 sun warke, 1,180 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,301 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 23,850, FCT –7,279, Oyo – 3,742, Edo –2,717, Delta –1,824, Rivers 3,045, Kano –1,819, Ogun –2,258, Kaduna –3,387, Katsina -1,064, Ondo –1,728, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi –782, Ebonyi –1,055, Filato – 3,914, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –681, Jigawa –336, Kwara –1,110, Bayelsa –458, Nasarawa – 521, Osun –947, Sokoto – 171, Niger – 298, Akwa Ibom – 358, Benue – 501, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 100, Ekiti – 377, Taraba- 175, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
A wani bincike da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gudanar ya nuna cewa 18.3% na mutanen da cutar korona ta kashe a Afrika na fama da cutar siga wato ‘Dibeties’ a daidai lokacin da suka kamu da cutar.
WHO ta gudanar da wannan bincike a kasashen Afrika 14.
Sakamakon wannan bincike ya nuna hadarin da masu dauke da ciwon siga ke ciki a wannan lokaci da annobar korona ta dabaibaye duniya musamman ga wadanda ke da shekaru 60 zuwa sama.
An gano cewa mutane da dama da ke dauke da wasu cututtukan sukan fada cikin yanayi na damuwa saboda maida hankali da aka yi kan kauda korona. Wasu cututtukan kuma suna ta cigaba da yaduwa.
Discussion about this post