Shugaban kungiya kiwon lafiya ta duniya WHO Tedros Ghebreyesus ya gargadi mutane su daina ganin kamar an gama da cutar Korona a duniya, ” har yanzu cutar na nan ta na ci gaba da yaduwa sannan mutane na ci gaba mutuwa a dalilin cutar.
Idan ba a manta ba kasar Birtaniya ta amince da maganin rigakafin cutar da kamfanin Pfizer da BioNTech suka hada har ma ta ce zata fara amfani da maganin nan bada dadewa ba.
haka kuma a cikin watan jiya an yi gwajin sanin sahihanci da ingancin maganin da hukumar MHRA ta yi a kan maganin ya kai kashi 95.
Kamfanonin za su fara yi wa mutane allurar rigakafin a cikin wannan wats na Disemba.
Kamfanin Pfizer dake kasar Amurka da Kamfanin BioNTech dake kasar Jamus suka Sanar cewa sun hada maganin rigakafin kamuwa da kwayoyin cutar korona dake da aka tabbatar da ingancin sa da akalla kashi 90 bisa 100.
Wadannan Kamfanonin sun hada wannan magani ƙasa da lokacin da ake zaton za a kammala hada shi kuma har sun yi gwajin ingancin sa a jikin mutane sama da 44,000.
Kamfanonin na sa ran cewa gwajin ingancin maganin da ake yi ba zai dauki tsawon lokaci ba domin samun izinin fara amfani da maganin
Discussion about this post