Dimokradiyya Tayi Abun Kunya A Najeriya, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Masana dimokradiyya sun tabbatar da cewa, an samar da ita ne don ta samarwa mutane farin ciki da ‘yanci daga hannayen shugabanni irin na gargajiya wadanda suke da karfin iko akan komai.

Ita kanta kalmar ‘democracy’, da yaren girka tana nufin “Gwamnatin mutane.”

A Najeriya, tun bayan dawowa mulkin dimokradiyya karo na 4, mutane sun sa ran samun sabuwar Najeriya, duba da yadda Allah ya tsareta ba tare da soja ya kuma tankwabeta ba kamar yadda aka saba gani a baya. Yau a akalla shekara 21 ana yin tsarin a Najeriya. Saidai shekarun basu amfana komai ba, idan aka duba irin damar da aka samu. Da kuma halin da ‘yan kasar suke ciki.

Tunda aka fara dimokradiyya a Najeriya, ake yin kamfen da wuta, ruwa, aikin yi, tsaro, titi, lafiya, ilimi da sauransu.

Wadannan abubuwan sune manyan matsalolin ‘yan kasar a yanzu. Abun tambaya a nan shine, mu ba zamu taba fita daga cikin rashinsu ba? Shin ina jam’iyar mutane? Ina jam’iyar canji? Ina bashin da muke karbowa daga waje tun 1999?

Gaskiya dimokradiyya tayi abun kunya a Najeriya. ‘Ya’yanta na kasar sun kunyatata. Taji jiki kuma ta fadi ba nauyi. Talaka ya kasa samun farin ciki, bayan ance ita gwamnatin mutane ce, daga mutane, kuma don mutane take rayuwa.

Tirrr! Ana bata mata suna a Najeriya don an kasa sarrafata wajen samar da cigaba. Abun kunya ne ace, ana yin dimokradiyya amma kuma abubuwa suna kara lalacewa.

Babu wani abu guda daya da za a nuna ace wai gashi an yi nasarar kafashi ko kirkiro shi kuma gashi miliyoyin talakawan Najeriya na amfana da shi.

Akullum dimokradiyya kara haihuwar ‘ya’ya take yi amma kuma miskinai, sannan bata yi musu tanadin komai ba sai dai duk wanda ya zo shima ga fili ga dokinan sai inda aka tsaya. Wahalar yau dabam ta gobe da bam.

Matsalar ruwan nan dai, ilimi, wutan lantarki da titunan da ake kamfen dasu bai canja ba duk da canjin da aka yi ikirarin shi za akawo don talaka yaji dadi.

Allah ya shiryar damu, Amin.

Share.

game da Author