Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba za ta nemi wuri ta zauna ta huta ba, har sai ta tabbatar da ta samo hanyoyin da za ta magance wadannan hare-haren ta’addanci da ake yi.
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya bayyana haka a ranar Talata.
Osinbajo ya yi maganar ne dangane da mummunan harin da Boko Haram su ka kai wa manoman shinkafa, har su ka kashe mutum 43 a Zabarmari da ke cikin Karamar Hukumar Jere, Jihar Barno.
Ya yi bayanin ne a lokacin da ya isa Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa domin wata ziyara.
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ne ya karbi bakuncin sa.
Osinbajo ya ce ya yi magana da Gwamnan Barno Babagana Zulum da kuma tsohon gwamnan jihar, Kashim Shettima, wadanda ya ce ya yi masu ta’aziyya, jajantawa da taya su alhini.
“Amma dai babbar magana mafi muhimmanci dai ita ce a lalubo hanyoyin da za a bi domin a magance irin wannan mummunan hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa.”
Ya ce lallai akwai bukatar a sake nazarin irin hanyoyin da ake bi wajen wannan yaki, a lalubo sabbin dabarun magance wadannan irin wannan harin sunkuru da Boko Haram ke kaiwa.
A ranar Talata ce Boko Haram bangaren Shekau su ka bada sanarwar daukar alhakin kai hare-haren kisan gillar da aka yi wa manoman su 43.
Sun ce sun yi masu ramuwar gayya ce saboda mazauna yankin na Zabarmari sun kama dan uwan su daya, sun damka shi ga sojoji.
Osinbajo ya ce kisan ba karamin ta’adddanci ba ne, kuma abin ya taba shi, ya taba zuciyar sa kwarai da gaske. Sannan kuma ya ce ya na mika ta’aziyya, alhini da jimami ga iyalan wadanda su ka rasa rayukan su.