Jami’ar East Carolina University dake kasar Amurka ta nada gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje farfesa na jeka ka dawo a jami’ar.
Idan ba a manta ba, an taba ganin gwamna Ganduje a wani bidiyo da aka dauka a asirci ya na karbar cin hancin daloli daga hannu wani ɗan kwangila ya dannawa a cikin aljihan jamfar sa.
Mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ne ya bankado wannan bidiyo, wanda BBC da Premium Times suka tabbatar da asali da sahihancin sa.
Duk da Jaafar ya bayyana a gaban majalisar jihar domin kare kansa da tabbatar da haka, gwamna Ganduje ya nemi a dakatar da sauraren wannan badakala bisa ga kariyar da yake mora a matsayin sa na gwamna.
Kotu ta amince da haka, ta dakatar da cigaba da binciken.
Ganduje da makarraban sa basu iya karyata wannan bidiyo har zuwa lokacin da aka dakatar da wannan bincike a majalisar jihar.
Ganduje zai rika zuwa jama’ar yana yin musayan ra’ayi da karantar da dalibai masu karatun PHD, kananan malamai da baiwa sashen bincike kan al’muran kasashen waje shawara.
Jami’ar ta ce ta zabi gwamna Ganduje cikin duka gwamnonin Najeriya, ganin wai shine ya fi jajircewa wajen yin tafiya da talakawan sa, sannan kuma da yi musu aikin azo a agani domin cigaban jihar sa, zuhudu da kuma kyamatar cin amanar jihar sa.