CASUN FASIKANCI: El-Rufai ya kwankwadi addu’o’i da fatan alkhairi daga mutane Kaduna

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya kwankwadi addu’o’i da fatan Alkhairi daga mutanen jihar, ganin yadda gwamnati ta gaggauta damke matasan da suka shirya bikin nuna tsiraici, fasikanci da iskanci a Kaduna.

Rahotanni sun nuna cewa tun bayan, fallasa wadannan matasa da aka yi, jami’an tsaro suka damko su, sannan aka garzaya otel din da ya basu wuri shi shirya wannan batsa, da tambadewa aka rusa shi.

Wannan himma na gwamnati ya yi matukar faranta wa mutanen kaduna rai sannan sun yaba wa gwamnan matuka na wannan abu da yayi.

” Idan da za a rika samun shugabanni masu fadin gaskiya da rikon amana, wadanda ba hassada, tsoro da munafunci a zukatan su kamar gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, da ba jihohi ba kasa Najeriya ta dau seti.

” Irin yadda gwamnatin Kaduna ta gaggauta damke matasan da ke kokarin gurbata tarbiyyan matasa ta hanyar shirya wani tambadewa ya faranta wa dimbin ‘yan Kaduna da ma na wajen Kaduna rai.

” Ace wai an wayi gari, wasu tambadaddun yara marasa tarbiyya, ‘yan iska, fitsararru, su fito karara a jihar Kaduna suna tallata irin wannan sharholiya da tambadewa sam sam bai dace ba. Amma kuma sun gamu da daidai su, ai ramin kura ba wajen wasan Kare bane, ga su ga El-Rufai nan, za su gwammace kidi da Karatu. Allah ya saka masa da Alkhairi.

Kama wadannan yara da aka yi da kuma rusa wurin da za a dabdale ya tabbatar da jajircewar gwamna El-Rufai na ganin lallai an tabbatar sannan an inganta tarbiyyar matasa a jihar.

El-Rufai kowa na shine, amma kuma kowa fa ba nashi bane idan ka nemi ka karya doka da kuma kawo wa gwamnati cikas a ayyukan ci gaba da ta saka a gaba don talakawan jihar Kaduna ko kuma kawo tambada irin haka.

Idan da ba irin su El-Rufai din bane, da kila wadannan matasa su sha.

” Ace wai an kai lokacin da za a rika tallata fasikanci kuru-kuru a tsakanin al’umma, wannan abu bai yi wa mutane dadi ba.

” Allah ya saka wa gwamna El-Rufai da Alkhairi kan wannan kokari da yayi sannan su kuma wadanda suka shirya wannan iskanci, tambadewa, ashararanci, fasikanci, lalacewa duk gwamnati ta yi maganin su saboda gaba, kai hatta wadanda bincike ya nuna suna basu goyon baya a bayyane ko a asirce, duk a lallasa su, a koya musu hankali.

” Wannan ya zama darasi ga irin wadannan algunguman matasa dake kokarin lalata al’umma.

Wannan sune kalaman Malam Mahmuda Muhammadu, a tattauna wa da yayi da PREMIUM TIMES HAUSA A Kaduna, ranar Alhamis.

Share.

game da Author