KORONA: Legas, Abuja da Kaduna suka fi yawan wadanda suka kamu ranar Jajibarin 2021 cikin mutum 1,031 da suka kamu

0

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –570, FCT-117, Kaduna-109, Nasarawa-34, Bauchi-31, Kano-28, Filato-26, Sokoto-26, Ogun-25, Edo-18, Ribas-16, Abia-10, Imo-7, Taraba-6, Delta-4, Osun-4.

Yanzu mutum 87,510 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 73,713 sun warke, 1,289 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,591 ke dauke da cutar a Najeriya.

A ranar Laraba, mutum 1016 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Kaduna, Filato, Ribas, Oyo da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 30,188, FCT –11,705, Oyo – 3,939, Edo –2,870, Delta –1,883, Rivers 3,475, Kano –2,262, Ogun–2,493, Kaduna –5,236, Katsina -1,618, Ondo –1,810, Borno –806, Gombe –1,272, Bauchi –1,009, Ebonyi –1,107, Filato – 4,875, Enugu –1,382, Abia – 1,015, Imo –755, Jigawa –403, Kwara –1,414, Bayelsa –534, Nasarawa –799, Osun –1,012, Sokoto –357, Niger – 413, Akwa Ibom – 434, Benue – 532, Adamawa – 391, Anambra – 312, Kebbi – 173, Zamfara –119, Yobe – 187, Ekiti –410, Taraba- 217, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.

Gwamnan jihar Kogi yahaya bello ya soki yadda gwamnatin Najeriya ta ke biye wa kasashen duniya game da annobar Korona da ake fama da ita a kasar nan da duniya baki daya.

Gwaman Yahaya Bello ya ce bai ga dalilin da zai sa gwamnatin Najeriya ta rika kashe makudan kudade da sunan wai ana yaki da yaduwar korona a kasar nan ba.

” Idan ana sanyi a kasashen Turai da Amurka suna saka kayan sanyi mu kuma a kasar nan muna saka kaya wanda ba na sanyi ba. A najeriya fanka da AC muke sakawa saboda zafi. Menene zai sa dole sai yadda turawa suke so muma a wannan yankin za miu yi.

” Ba mu da cutar Korona a jihar Kogi saboda haka ba za mu kirkiro ta da karfin tsiya ba. Kuma mun yi wa mutane da dama gwaji a jihar mu, babu wanda aka samu ya kamu da cutar a jihar.Bamu da Korona wani ba zai zo ya hakikance ewa sai dole mun ce muna da masu cutar ba.

” Idan aka ce za a rika yi wa mutane Kulle, wato zaman gida dole, za a yi ta samun matsala, mutane za su rika mutuwa saboda wahala. Korona Kasuwanci ne kawai ake yi da ita wanda mu bamu bukatar irin wannan kasuwancin a kasar nan, kawai sai narka kudade kae yi da sunan wai dakile yaduwar Korona.

Gwamna Yahaya ya kara da cewa a yanzu haka ana cewa za a tara naira biliyan 540 don siyo maganin rigakafin cutar. wanda da ayyukan raya kasa aka saka wa da an samu ci gaba a akasar nan.

” Ina gina katafaren asibiti a jihar Kogi, mun kiyasta za mu kashe naira biliyan 4.6. Idan za a kashe wa kowacce jiha a kasar nan naira biliyan 10 akalla, don gina irin wannan asibiti, da mun ciwo karfin wahalhalun rashin lafiya da mutanen mu ke fama dashi maimakon muje mu siyo wa kan mu gaibi.

” Korona ko da magani ana warkewa idan dai ba wata matsala aka samu ba. Haka kuma Bankin Kasa ya bayyana cewa an kashe sama da naira Tiriliyan 3 wajen yaki da korona a kasar nan, wadannan kudade da ayyukan cigaba a ka yi a kasa da yafi.

Share.

game da Author