Gwamatin Kaduna ta rusa Otel din da za a yi casun tabdalewa da nuna tsiraici da fasikanci dake Unguwar Barnawa dake Kaduna.
Idan ba a manta ba Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta kama matasan da suka shirya sharholiyar gwangwajewa tsirara a Kaduna ranar 27 ga Disamba.
Wasu matasa sun shirya bikin sharholiya da fasikanci tsakanin mata da maza a garin Kaduna domin murnar karshen shekara.
Matasan sun saka katin gayyata da tallata sharholiyar a shafin Facebook, inda suka saka wasu sharudda da suka hada da wai duk mai son halartar gwangwajewar ya zo wurin babu kaya a jikin sa, wato tsirara haihuwar uwar sa.
Bayan nan ya tabbata ya zo da kororo roba, domin za a tafka fasikanci ne tun daga karfe 8 na dare zuwa washe garin ranar 28.
Domin shiga wurin gwangwajewar, mai bukatar haka zai biya naira 1000, sannan akwai wurare na musamman da za a biya naira 2000 zuwa naira 5000.
Sai dai kash, wannan haka ta su bai kai ga ruwa ba, domin jami’an tsaro sun farwa masu hada wannan shu’umanci inda suka bi sahun su har Allah ya sa suka damke wasu saga cikin masu shirya wannan sharholiya.
Daya daga cikin maiba gwamnan Kaduna shawara kan harkokin yada Labarai, Abdallah Abdallah, ya rubuta a shafinsa ta tiwita cewa yayi matukar farin cikin damke wadannan yara da aka yi.
Mazauna Kaduna kuma sun yi tofin Allah-Tsine ga wadanda suka shirya wannan biki, suna masu godewa jami’an tsaro kan saurin kama wadannan yara da suka yi.
Discussion about this post