Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 108 cikin sati daya a Arewa maso Yamma

0

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta bayyana cewa sojoji sun bindige mahara masu garkuwa da mutane kimanin 108 cikin mako guda, a yankin Arewa maso Yamma, da kuma burbushin wasu ‘yan Boko Haram a Arewa maso Gabas.

Kodinatan Tsaron Najeriya John Enenche ya bayyana haka a lokacin da ya ke bada bayanin sararorin da sojoji su ka samu mako-mako, na ranakun 19 zuwa 25 Ga Nuwamba, ranar Alhamis, a Abuja.

A yankin Arewa maso Yamma, Manjo Janar Enenche ya ce Dakarun Operation Hadarin Daji sun gudanar da hare-hare sosai ta sama, ta kasa da kuma yin rubdugun ruwan wuta a wasu sansanonin ‘yan bindigar da aka yi wa takakkiya, aka kifar da su baki daya.

Ya kara da cewa baya a kashe masu yawan gaske, an kama wasu tare da munafukai da magulmatan da ke hada kai da su, su na ba su rahotannin mutanen da za su kama su yi garkuwa da su.

Ya a Dajin Birnin Kogo na Katsina da kuma Dajin Ajjah da ke Zamfara, can ne sojoji su ka yi wa ‘yan bindiga 82 luguden wutar da aka markade su, kowa ya huta.

Ya ce an samu wannan gagarimar nasara a Birnin Kogo da Ajjah a ranar 24 Ga Nuwamba.

Manjo Janar Enenche, ya ce sojojin sama sun kashe ‘yan bindiga 17 da Dajin Dunya cikin Jihar Katsina.

Ya ce an kai hare-haren ne bayan samun rahoto sahihi cewa akwai wasu ‘yan ta’addar Ansaru da su ka yi kakagida a dazukan. Bayan kashe su an kuma samu shanu masu yawa wadanda su ka kama a hare-haren da su ke kaiwa kauyukan jama’a.

Ya kara da cewa an kama mutum 11 masu hako ma’adinai.

Enenche ya ci gaba da bayar da bayanan nasarorin da aka samu a sauran jihohi, har da jihar Benuwai.

Share.

game da Author