Kashe-kashe sun yi muni a Arewa, a yi zaman lalubo mafita – Sultan Sa’ad

0

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya ce kashe-kashe a Arewa sun yi munin da a yanzu haka mutane na tsoron yin tafiye-tafiye.

Ya yi wannan tsokacin ne a taron Majalisar Tattauna Al’amurran Addinai zango na hudu da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Sarkin Musulmi ya ce matsalar tsaro ta yi tsanani a Arewa har ta kai mutane na tanadar kayan abinci su na ajiyewa a gidajen su, saboda masu garkuwa da mutane.

Daga nan sai ya yi kira a taron kasa domin tattauna yadda za a shawo kan wannan matsala.

“Akwai bukatar gaggawa ta a hanzarta a zauna a magance wannan gagarimin bala’i. Domin akwai mutane masu kishi wadanda za su iya bayar ta shawarwari na kwarai.” Inji Sultan.

“Babbar matsalar mu ita ce ba a son yin aiki tsakani da Allah. Kowa kan sa ya ke so. Wannan babbar matsalar mu ce.”

Sultan ya kara da cewa akwai bukatar duba matsalar kayan abinci a kasar nan. Babban abin haushi da abin dariya, ya ce shi ne yadda farashin albasa ya ke neman ya zama kamar farashin gwal.

“Tsadar farashin albasa a kasar nan, ya na nuna irin gagarimin matsalar abincin da tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar nan.”

Daga nan ya roki ‘yan Najeriya su daina lalata kayayyakin gwamnati ko na sauran jama’a.

Da ya ke bayani, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya yi kira ga shugabannin addinai su ci gaba da yi wa kasa addu’a.

Shi kuwa Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa. CAN, Samson Ayokunle, ya ce abin da ya haifar da tarzomar #EndSARS a kasar nan, abin takaici ne matuka.

Share.

game da Author