BINCIKEN KWAKWAF: Shin da gaske Gwamnatin Katsina ta salwantar da biliyan N52.6 kan matsalar tsaro?

0

Shin da gaske ne batun da ke yawo cewa gwamnatin jihar Katsina ta salwantar da naira biliyan 52.6 da sunan yaki da matsalar tsaro a jihar?

Jaridar nan ta yanar gizo ta DAILY NIGERIAN ta gudanar da binciken kwakwaf akan lamarin. Ga rahoton da ta fitar:

ZARGI:

Wani dan kasuwa mazaunin jihar Kaduna kuma haifaffen Jihar Katsina mai suna Mahdi Shehu, ya yi ikirarin cewa Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin Gwamna Aminu Bello Masari ta kashe Naira biliyan 52.6 da sunan tsaro a jihar.

ABIN DA AKA TABBATAR: Binciken ƙwaƙƙwafi kan takardun ya nuna cewa iƙrarin ba shi da tushe. Domin takardun da aka kafa hujja da su kan iƙrarin suna da alamomin tambaya da rashin gamsarwa. Saboda haka mun gano cewa wannan iƙrari QARYA ne.

BAYANI:

A ‘yan kwanakin nan Mahdi Shehu ya yi fice wajen zama mai sukar gwamnatin jihar Katsina da wasu daga jami’anta. Ya kan raba takardun da ke zargin yadda gwamnatin Aminu Masarin ke fitar da kuɗi ba bisa ƙa’ida ba. Malam Mahdi ya kan yin hakan ne ta hanyar jawabi namsauti da kuma bidiyo da ake watsawa a dandalin sada zumunci kamar su WhatsApp.

A baya wasu jaridu sun kawo rahotanni kan zargin na Mahdi Shehu da jawabin kariya na gwamantin Katsina, har ma da gayyatar da jami’an tsaro sauka yi masa domin tuhumar zargin da yake yi.

A cikin watan Satumba hukumar tsaro ta farin kaya ta gayaci Madi ofishinta dake Kaduna.

An gayyaci ɗan kasuwar ne domin ya amsa tambayoyi kan manya-manyan zargin da yayi kan waɗanda ya zarga da sace dukiyar jihar. Daga cikin waɗanda ya ambata akwai babban hafsan hafsoshin soja, Laftanar Janar Tukur Buratai.

Kuɗaɗen da ya ambata cewar ana fitarwa duk wata da ya kai jumillar Naira biliyan 52.6 abin matuƙar mamaki ne da tada hankali.

Jihar Katsina na cikin jihohin da ke fama da matsalolin hare-haren ‘yan ta’adda a yankin arewa maso yamma ta yadda mutane ɗauke da muggan makamai ke afkawa ƙauyuka suna aikata fashi da ƙwace da kuma garkuwa da mutane. Wannan ne karon farko da aka samu haka a jihar da a baya ta shahara wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kodayake harkar tsaro na ƙarƙashin rataye na ɗaya na Kundin Tsarin Mulki na Najeriya, ma’ana haƙƙin gwamnatin tarayya ne, jihohi da sunan tsaro suna ba da gudummawar kuɗaɗe da kayan aiki wajen ɗaukar nauyin jami’an tsaron tarayya kamar ‘yan sanda da sojoji da sauransu.

Gwamnonin jihohi suna kokawa game da yadda nauyin samar da motocin aiki da sauran kayan aikin ‘yan sanda da sojoji ke kara zama nauyi a kansu. Wannan yana taka rawa sosai wajen zuƙe kudade jihohi domin dole su taimaka wajen samar da tsaro.

BIN DIDDIGIN IƘRARIN

Duba na tsakani kan takardun da Malam Mahdi yake yaɗawa ya nuna lauje cikin naɗi da rashin ƙwarewa. Takardu ne barkatai da ake nuna cewar wai umarni ne daga ofishin sakataren gwamnatin jihar, watau abin da ake kira ‘memo’. Waɗanda ke nuna cewar a fitar da kuɗaɗen daga asusun tsaro na gwamnatin jihar. Dukkanin takardun ana zargin cewar sun fito ne daga Sashen Kasafin Kudi da Tsara Tattalin Arziki kuma da sa hannun wani jami’i mai suna Bature S.N. Danlami.

SHAIDA TA ƊAYA:

Saɓanin iƙirarin da Malam Mahdi ya yi a jawabansa da kuma takardun da ke zagayawa tsakanin al’umma, cewa Asusun Tsaron Gwamnatin Jihar ba ya cikin Bankin Fidelity. Lambar asusun bankin Fidelity da ake yaɗawa ya kasance na wani sabon asusu ne da aka buɗe a watan Yuni domin tattara kuɗaɗen da aka yi gwanjon kadarorin gwamnati. Daga sahihin bayanin da aka samo na wannan asusu, ya nuna cewar ba a taɓa fitar da kuɗi daga cikinsa ba.

SHAIDA TA BIYU:

Takardun da Malam Mahdi ke yaɗawa bisa zargin kashe kuɗaɗen tsaro na ƙunshe da suna da tambarin hukuma ɗaya da kuma sa hannu guda biyu na Bature S.N. Danlami. Wani abin mamaki, duk da takardun na ɗauke da sa hannu bibbiyu, amma dukkansu iri ɗaya ne babu bambanci. Wannan ya haifar da ɗiga babbar ayar tambaya kan irin wannan nannauyan zargi da ake buƙatar ƙwaƙƙwarar hujja, amma sai ga shi dukkan takardun suna ɗauke da sa hannu iri ɗaya asin da asin ba tare da kuskure ba. Abu ne mai wahala mutum ɗaya ya riƙa sa hannu a takardu iri daban daban har tsawon shekaru uku (3) daga 2018 zuwa 2020 amma ya zamana duk iri ɗaya ne tsawonsu da faɗinsu da kaurinsu.

SHAIDA TA UKU:

Ƙwaƙƙwarar shaidar da jaridar nan ta samu ya nuna cewar dududu kuɗin da gwamnatin ta kashe wajen motocin aiki ga jami’an tsaro gami da alawus ɗin da aka bayar ta fuskar tsaro a shekara biyar shi ne N5,085,714,929. A cikin adadin, kamar yadda wakilinmu ya gani, ya nuna cewar an kashe N1,279,354,170 a shekarar 2019 wanda shi ne mafi qololuwa a wannan a dukkan shekarun nan guda biyar. Wannan kuwa ya faru ne kasancewar shekarar ce aka samu ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga, wanda ya kai ga jibge dakarun sojoji a jihar domin samar da tsaro.

KAMMALAWA

Daga shaidun da muka samu, ta tabbata cewar zargin ɓarnatar Naira biliyan 52.6 kan harkokin tsaro a jihar Katsina, labari ne na ƙanzon kurege da ba zai zama abin dogaro ba saboda hujjojin da aka gabatar basu da inganci.

Share.

game da Author