Ba a taba kirkiro shirye-shiryen kawar da fatara da talauci a Najeriya kamar yadda Buhari ya yi ba -Lai Mohammed

0

Tsare-tsaren kawar da fatara da talauci da Shugaba Muhammadu Buhari ya kirkiro musamman ga mata da marasa galihu, babu wata gwamnatin Najeriya da ta taba ko kwatanta hakan a Najeriya.

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka a Kaduna, a taron da gwamnonin yankin Arewa su ka yi tare da sarakunan gargajiyar yankin, bayan tarzomar #EndSARS.

Ministan ya shaida wa mahalarta taron a matsayin sa na mamba din cikin tawagar gwamnatin tarayya a wurin taron.

Ya ce gwamnatin Buhari ta maida hankali sosai wajen fito da tsare-tsaren samar wa matasa aiki da kuma kawar da talauci.

“Tun bayan kafuwar Najeriya babu wata gwamnatin da ta taba ko kwatanta irin ayyukan da gwamnatin Buhari ta yi wajen kawar da fatara da talauci da samar da ayyukan yi.” Inji Lai.

Ya fara da buga misali da Shirin Bunkasa Jarin Matasa da Naira Bilyan 75, wato NYIF da ake kokarin fara aiwatarwa a yanzu.

Ya ce kudin na daga cikin Shirin Ceto Tattalin Arzikin Kasa da gwamnati za ta kashe naira tiriliyan 2.3 wajen tallafa wa kanana da matsakaitan masana’antu, bayan da cutar korona ta dagula harkokin tattalin arziki a kasar nan da sauran kasashen duniya.

Ya ce tun cikin watan Yuli 2020 Majalisar Zartaswa ta Kasa ta amince a tallafa wa matasa daga masu shekaru 18 zuwa 35. Ya ce shirin zai dauki shekaru uku ana gudanar da shi daga 2020 zuwa 2023.

Kwanan nan Buhari ya ce akalla matasa milyan daya ne su ka cika fam na neman tallafi daga naira bilyan 75 din da za a raba a karkashin shirin NYIF, wanda aka fara cika FAM din sa a ranar 12 Ga Oktoba, 2020.

Daga nan Lai ya ci gaba da lissafo sauran ayukan inganta rayuwar jama’a da tallafi ga marasa galihu.

Share.

game da Author