Kimanin ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomin jihar Barno 38, ciki har da masu mukamin Farfeso a jami’o’i biyu, za su fafata a zaben da za a yi ranar Asabar a jihar Borno.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Borno (BOSIEC) ce ke shirya zaben.
Mazauna Jihar Borno, a karon farko cikin shekaru 13, za su zabi jami’ai na kananan hukumomin 27 da ke jihar.
Wannan shine karo na farko da za a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Barno tun 2012, shekaru 13 kenan.
Tun lokacin da aka zabi jami’an a watan Afrilun 2012, lokacin ne jihar ta gudanar da zabukan kananan hukumominta na karshe. Tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu kantomomi ne gwamnatocin da suka wuce syka nadawa.
Shugaban Hukumar zabe na jihar Abdu Usman ya shaida cewa jam’iyyu sun mika ‘yan takaran shugabannin kananan hukumomin 39 sannan kuma akwai ‘yan takarar kujerun kansiloli 318 da za su fafata a zaben.
Akwai Farfeso biyu daga kananan hukumomin Gwoza da Damboa da suma sun fito takara.
18 daga cikin kananan hukumomi 27 sun mika ‘yan takara daya tilo ne babu abokin hamayya. A dalilin haka ba za a yi zabe a wadannan kananan hukumomi ba. Za a yi a 11 ne kawai wadanda akwai abokanan hamayya, wato ‘yan takara a wasu jam’iyyun.
Za a fara zabe da karfe 8 na safe ranar Asabar, sannan a gama da misalin karfe biyu na rana.