Ina taya Umahi murnar wancakalar da PDP da ya yi ya koma APC – Matawalle

0

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa gidan da ake maraba da kai nan ne za ka samu kwanciyar hankali ba inda duk da ana tare amma kuma ana yi maka zagon kasa ba.

A wata takarda wanda kakakin sa ya saka wa hannu, Zailani Bappah, Matawalle ya ce kwata-kwata PDap yanzu sai a hankali, babu hadin kai sai tsangwama kawai a tsakanin mambobinta.

” Umahi ya ga cewa APC ne zai samu kwanciyar hankali, shiya sa ya sauya sheka, ya fice daga PDP ya koma APC. Bakin jinin da PDP ke yi yanzu idan ba a gaggauta yin wani abu akai ba za a kwan ciki yanzu da ake tunkarar 2023.

” Kamar ni Yanzu bana jin dadin yadda ‘ywn uwana gwamnonin PDP suke yi min, abin yana bani mamaki matuka. Ace wai gwamnonin yankin Kudu Maso Kudu, wanda duk yan PDP ne amma kuma sune suka caccakata a kafafen yada labarai saboda gwal din dake dankare a Zamfara.

” Abin ban mamaki, gwamnatin APC ne ke kare ma, syke ja da gwamnonin PDP din, maimakon ace tunda ana tare cikin jam’iyya daya su ne me ni tukunna, mu tattauna, su san ainihin maganan amma kuma suka ci mini mutunci karara a kafafen yada labarai.

” Na yi matukar gode wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa daman da ya bani sannan da goyon baya tunda aka fara kai ruea rana game da maganan gwal din.

” Gwamnatin Zamfara bata da iko akan ma’adinan dake karkashin kasa a jihar. Mallakin gwamnatin tarayya ne. Kuma gwamnatin tarayya ta ba da lasisi ga kamfanonin da zasu rika yi mata aikin hako ma’adinan a kasa.

Matawalle ya ce Kamfanin wani dan Kabilar Igbo ne kuma dan asalin jihar Anambara ke da kaso.mai tsoka a harkar aikin hako ma’adinai a jihar cikin kamfanonin da ak basu lasisi.

Share.

game da Author