Gwamnan jihar Barno, Babagana Zulum ya bayyana cewa dole sai sojojin Najeriya sun canja salon yaki da Boko Haram sannan ne za su yi iya nasara a kan su.
Zulum ya ce idan dai har ana so a yi galaba akan Boko Haram, dole sai ana tunkaran su gaba-da-gaba ne abi su har can ida suke a boye a gama da su, ba a rika jiran sai sun kawo hari ba.
” Amma idan wai ace za a rika jiran su ne sai sun afko wa sojoji ko mutane sannan a fafure su to ba za a gama da wannan matsala ba. Sannan kuma wani abu da zai yi matukar tasiri shine idan ana zabo zakakumen sojojine ana tura su wuaren arangama da ‘yan ta’adda ba kowa ba kawai.
Zulum ya kara da cewa gwamnatin sa a shirye ta ke ta ci gaba da mara wa rundunar sojin baya domin samun nasara akan yaki da Boko Haram da suke yi a jihar da yankin baki daya.
A na shi jawabin, babban hafsan sojojin Najeriya Tukur Buratai ya mika godiyar sa ne ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Barno Bababgana Zulum wajen kokari da suke yi na ganin sun mara wa sojojin baya ta kowace hanya da suke yi don ganin an kawo karshen Boko Haram a kasar nan.
” Duk da annobar Korona ta kawo mana cikas a ayyukan da muka so mu zartar a wannan shekara, 2020, zan iya bugun kirji ince duk da haka an samu nasarori da dama.
A karshe Buratai ya ce rundunar soji zata gina sabbin gidaje domin iyalan sojojin da suka rasu a filin daga.