A ranar Talata ne shugaban asibitin Abuja, Jaf Momoh ya yi kira ga mata da su rika zuwa asibiti domin yin gwajin cutar dajin dake kama nono cewa gano cutar da wuri na sa a warke daga cutar.
Momoh ya fadi haka ne a taron da kungiya mai zaman kanta ‘Breast Imaging Society of Nigeria (BISON)’ ta shirya domin wayar wa mata kai game da mahimmancin zuwa asibiti idan aka samu matsala da nono tun da wuri.
Bayan haka shugaban daukan hoto na asibitin Feyisayo Daji, ta yi Kira ga mutane masu shekaru 40 zuwa sama da su rika yin gwajin cutar akalla sau daya bayan shekara biyu.
Feyisayo ta kuma kara da cewa wadanda shekarun su bai kai 40 ba za so iya zuwa asibiti domin a dauki hoton nonon su sannan wadanda suka dara shekaru 50 za su rika yin gwajin cutar duk shekara.
Ta Kuma bada shawara ga mata da su rika duba nonon su lokaci-lokaci domin gano alamun cutar a nonon , idan kuma suka ji ba daidai ba sai su garzaya asibiti cikin gaggawa.
Wasu likitocin da suka kware kan cutar daji da lafiyar yara a kasar nan sun bayyana cewa shayarwa da mulmula nona baya hana kamuwa da cutar dajin dake kama nono kamar yadda ake ta camfawa.
Bamidele Iwalokun shugaban likitocin ya bayyana cewa sun gano haka ne a bincike da suka gudanar don gano haka.
Iwalokun yace sakamakon binciken ya nuna cewa mulmula nono na sa kwayoyin cutar a nono kara girma yadda ya kamata sai dai kuma hakan na taimaka wa wajen gano cutar da wuri.
” Mutane sun dauka cewa shayarwa ko mulmula nono na kare mace daga kamuwa da wannan cutar amma bisa ga wannan bincike mun sami tabbacin cewa lallai ba haka bane.
” Mata da suka kamu da wannan cutar mazajen su ne ke fara ganowa kafin mu likitoci mu sani.”
Iwalokun ya yi kira ga mata da su dage wajen shayar da ‘ya’yan su, mulmula shi akai akai, cewa hakan na taimakawa wajen bada tazarar iyali, rage kiba, kare mace da kamuwa da hawan jini, kara dankon zumunci tsakanin uwa da ‘da.