Hankalin Buhari bai girgiza dalilin masu hauragiyar a sauya fasalin Najeriya ba – Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai tashi hankalin sa ba, saboda hauragiyar da wasu da ya kira marasa kishi ke yi, cewa a sauya fasalin Najeriya ko kuma kasar ta tarwatse.

A ranar Lahadi ne Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar da sanarwar cewa masu wannan hauragiya ba su isa su raba wa Buhari hankali ba, musamman a wannan lokacin da ake fuskantar kalubale a bangaren lafiya.

Shehu ya fitar da wannan raddi ne bayan Shugaban Cocin RCCG, Enoch Adeboye ya yi kiran cewa ko da a sauya fasalin Najeriya, ko kuma kasar ta tarwatse.

Adeboye ya fadi ra’ayin da wasu manyan kasar nan, irin su Babban Sakatare na Ife, Ooni Adeyeye Ogunwusi, Tsohon Gwamnan Cross River, Donald Duke da Oby Ezekwesili su ka yi karaji a kai.

Adeboye ya ce, “shin me zai hana a sake fasalin Najeriya, yadda za a samu dunkulalliyar Najeriya. Saboda kowa ya san abin da ake nufi da sauya fasali. Ko dai a sauya fasalin Najeriya ko kuma kasar ta tarwatse.”

A raddin sa, Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari ba zai bada kai borin wasu ‘yan hauragiya masu yi masa barazana ya hau kan sa ba.

“Domin abin da su ke yi barazana ce, saboda har lokaci su ke shata wa Shugaban Kasa ya yi wani abu da son ran su ke nema, saboda wata boyayyar manufa.

“Shi kuwa Shugaban Kasa ba na wasu ‘yan tsirarun mutane ba ne. Akwai nauyin sama da mutum milyan 200 a kan sa. Kuma su ya ke yi wa ayyukan da ya yi alkawarin gudanarwa kamar yadda doka ta tanadar.

“Babu wasu tsirarun da za su iya karkatar da hankalin Shugaba Buhari, musamman a lokacin da kasar nan ke fama da barazana a fannin lafiya.” Inji Shehu.

A na sa bayanin, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi, ya ce sake fasalin Najeriya abu ne da sai an matakan ka’ida an koma a Majalisar Kasa tukunna.

Ya ce tsarin federaliyya din dai shi ne ya fi dacewa da Najeriya.

Share.

game da Author