Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Ondo, Leo Ikoro, ya tabbatar da cewa an yi yamutsi tsakanin magoya bayan APC da na PDP a ranakun Asabar da Lahadi a Jihar Ondo.
PREMIUM TIMES ta buga labari a safiyar Lahadi cewa gwabzawar da bangarorin biyu su ka yi a Lahadin, ta biyo bayan yamutsin da ya faru ne a ranar Asabar, inda aka yi an kashe wani dan jam’iyyar APC na yankin unguwar Oba Nla a Akure, a ranar Asabar.
A fadan da aka yi ranar Lahadi, magoya bayan bangarorin biyu sun rika ragargaza motocin masu ababen hawa a kan titin Oba Adesida.
Hakan ya sa tilas masu motocin sufuri suka rika canja hanya.
Ikoro ya ce ‘yan sanda sun kwantar da yamutsin kuma komai ya koma daidai.
Kakakin Yada Labarai na Kamfen din dan takarar APC, Rotimi Akeredolu, Mai suna Richard Olatunde, ya dora laifin a kan magoya bayan PDP.
Shi ma Kakakin Yada Labarai na Kamfen din dan takarar PDP Ayetayo Jegede, mai suna Kayode Fasua, dora laifin ya yi a kan magoya bayan APC.
Tuni dai Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, ya bada sanarwar tura Mataimakin Sufeto Janar da Kwamishinan ‘Yan Sanda 11 a Ondo, domin tabbatar da tsaro a lokacin zabe.
Hukumar Tsaron Sojoji ta tabbatar da cewa za ta tura dakaru 600 domin tabbatar da zabe cikin lafiya.
PREMIUM TIMES HAUSA ta ga yadda tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso ke taya dan takarar PDP kamfen a Ondo, a ranar Lahadi.
Dubban magoya bayan PDP sanye da jajayen huluna sun yi dandazo a wurin kamfen din, yayin da mawakin Kwankwaso, Tijjani Gandu ke kan mimbari ya na rera wakokin dan takarar PDP Ayitayo Jegede.