Shugaba Muhammdu Buhari ya rattaba hannun amincewa a kara wa malaman makaranta albashi.
Wannan ya na cikin sakon sa na yau Ranar Malaman Makaranta ta Duniya (World Teachers Day) a Abuja.
Ministan Harkokin Ilmi, Adamu Adamu ne ya wakilci Buhari a wurin taron, inda ya kara albishir din cewa an kara wa malaman wa’adin dadewa ana koyarwa kafin a yi ritaya, daga shekaru 35 ana aiki zuwa shekaru 40.
Buhari ya ce an yi karin domin a kara karfafa wa malaman makaranta karfin guiwar koyarwa a wannan mawuyacin halin annobar cutar korona da ya addibi duniya.
Wannan kari ya zo daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke tabka kirimirmirar rikici a kan batun biyan albashi a karkashin tsarin ‘yar keke-da-keken biyan albashi, wato IPPIS.
A yanzu dai gwamnati ta bayyana ranar komawar ‘yan makarantar firamare da daliban sakandare.
Sai dai ba gaba dayan su ne za su koma lokaci daya ba.
Mu na dauke da dalla-dallar irin karin da za a yi wa mai karamin albashi da kuma masu daukar albashin koyarwa mai nauyi.