A wani taron da Kungiyar Kwadago ta yi da wakilan Gwamnatin Tarayya da Kwamitin Saisaita Farashin Lantarki, an amince gwamnati za ta sassauta farashin kudin wutar lantarki da ragin naira 10.20 tsawon watanni uku.
Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo ne ya bayyana haka bayan kammala taron, wanda ya shugabanta.
Sun fara taron daga ranar Lahadi, tare wakilan Kungiyar Kwadago ta NLC da ta TUC, aka kammala Litinin.
Sauran yarjejeniyar da aka kulla, ta hada da raba wa jama’a milyan shida mita kyauta, makonni biyu da shan sassaucin wutar.
Sai dai kuma sassaucin kudin wutar, za a yi shi ne ga wasu ba’arin mutane, ba game-gari ba ne na bai-daya.
An kuma amince a tabbatar an kare tare da tsare albashin dukkan ma’aikatan kamfanonin saida wutar lantarki.
Kuma za a maida wa jama’a duk kudaden da aka caje su fiye da farashin lantarki na ainihi.
Alkawarin Shan Wuta Kyauta Na Baya:
Idan ba manta ba, a cikin watan Afrilu, farkon fara zaman korona, an yi alkawarin cewa a sha wutar lantarki kyauta tsawon watanni biyu.
A wani abu mai kama da abin da Hausawa ke cewa, ‘albarkacin kaza kadangare ke shan ruwan kasko, kamfanonin sayar da wutar lantarki wato Distribution Companies ko DisCos a takaice, sun bada sanarwa cewa za su bar kowa ya sha wutar lantarki kyauta tsawon watanni biyu.
Wannan kuwa wata gagarimar gudummawar su ce da suka ce za su bayar wajen taimaka wa gwamnati ta saukake wa jama’a radadi da kuncin zaman gidan da ake ciki domin kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus.
Babban Daraktan Bincike da Wayar da Kai na Kungiyar Kamfanonin Raba Wutar Lantarki ta Kasa (ANED), Sunday Oduntan ne ya fitar da wannan sanarwa a Abuja.
Ya ce ya kamata a hada hannu da gwamnati domin ganin an saukake wa jama’a halin kuncin da suke gida, na zama wuri daya cikin rashin kudi.
Ya ce nan ba da dadewa ba za a fitar da tsare-tsaren yadda kowa zai sha wutar kyauta.
Garuruwa da dama sun nuns rashin jin dadin yadda su ke fama da wuta a cikin wannanawuyacin halin da aka tilasta zaman killace kowa a gida, saboda Coronavirus.
Fitowar da wasu mazauna wasu unguwanni suka yi Lagos su na zanga-zangar rashin wuta, ta sa Kakakin Majalisar Tarayya ya gana da Ministan Harkokin Makamashi, Saleh Mamman cikin makon da ya gabata.
Ministan ya yi masa alkawarin za a Cuba lamarin domin a rika samun wuta ta na wadatar jama’a.
Bayan wannan a ganawar da Majalisar Tarayya ta yi da Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed, Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ya nemi a kafa kudirin dokar da za ta bada dala ‘yan Najeriya su sha wutar lantarki kyauta tsawon wata biyu.
Wannan sanarwa ta zo kwanaki uku bayan Shugaban Kasar Ghana ya na da umarni kowa ya sha ruwan famdo kyauta tsawon watanni uku a kasar, saboda rage wa jama’a kunci a lokacin zaman kadaicin rashin fita neman abinci saboda Coronavirus.
Ya kuma bada umarnin kada a dauke wuta tsawon watanni uku a kasar.