Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Hadimar Musamman Kan Soshiyal Midiya, Lauretta Onichie mukamin Kwamishinar Hukumar Zabe ta Kasa, mai wakiltar Jihar Delta.
Sauran su ne Mohammed Sani da zai wakilci Jihar Katsina, Kunle Ajayi wanda zai wakilci Jihar Ekiti, sai Saidu Ahmed mai wakiltar Jihar Jigawa.
Wannan sanarwar nadi ta na cikin wasikar da Buhari ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan.
Lawan, wanda ya karanta wasikar a Zauren Mahalisar Dattawa din, ya ce wasikar ta nuna Buhari ya nada su ne bisa ka’idar Doka ta 14, Sashe na 15 1f, na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
Cikin wata wasikar kuma, Buhari ya nemi amincewar Majalisa da nadin wasu Manyan Daraktoci uku da ya yi a Hukumar Kula da Gyaran Titina ta Kasa (FERMA).
Sun hada da Ifeanyi Christian daga Kudu maso Gabas, Muhammad Gambo daga Arewa maso Gabas sai kuma Abubakar Ismaeel daga Arewa maso Yamma.