Buhari ya kara wa shugaban INEC Mahmood Yakubu wa’adin shekara biyar

0

Shugaban Muhammadu Buhari ya kara ba Farfesa Mahmood Yakubu matsayin Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), bayan cikar wa’adin sa na farko.

A cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, Shugaban Kasar ya ce ya yi nadin ne a bisa tanadin Sashe na 154 (1) na Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya, na shekarar 1999 (kamar yadda aka gyara shi).

A wasikar, ya faɗa wa majalisar a yau cewa, “Ina farin cikin gabatar da zaben Farfesa Mahmood Yakubu, domin amincewar Majalisar Dattijai, don a nada shi Shugaban Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) a karo na biyu kuma na karshe.”

Shi dai Farfesa Yakubu, Shugaba Muhammadu Buhari ya soma nada shi shugaban hukumar ne a cikin watan Nuwamba na 2015.

A wannan sabon wa’adin ma, zai yi shekara biyar kamar yadda ya yi a na farko.

Yakubu ya gaji Farfesa Attahiru Jega, wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada.

Jega ne ya gudanar da zaben 2011 wanda Jonathan ya yi nasara a kan Buhari. Kuma shi ya shirya zaben 2015 da Buhari ya yi nasara kan Jonathan.

Wannan karin wa’adi ya nuna Yakubu ne zai shirya zaben 2023.

Share.

game da Author