Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Barcelona ya yi murabus bayan magoya bayan kungiyar sun ce ba su son sa a kujerar.
Bartomeu tare da manyan darektocin kolub din sun ajiye aiki ranar Talata.
Barcelona ta shiga rudani tun daga kakar kwallon kafa ta bara, inda kungiyar Bayern Munich ta lallasa ta da zura kwallaye har Takwas a ragar ta.
Sannan a wannan kakar kwallon kafa ne Barcelona ba ci ko da cokali bane ballata kofi a shekarar.
Sannan kuma rigimar barin kungiyar kwallon kafar da ya barke tsakanin sa da shahararren kungiyar kwallon kafar Leo Messi.
Messi ya ne mi ya bar kungiyar a bara, amma kuma Bartomeu ya ki bayan sun yi alkawarin cewa idan ya tashi tafiya zai amince masa.
Sannan kuma a karshen makon da ya gabata Kungiyar Real Madrid ta lallasa Barcelona din da ci uku da daya. Hakan ya dada fusata magoya bayan kungiyar da wasu dake bin kungiyar.