An gano wani kamfanin kasar Indiya dake saida jabun maganin ‘Ciprofloxacin’ Inji NAFDAC

0

Hukumar NAFDAC ta gargadi mutane da su yi takatsantsan wajen siyan maganin cutar ‘Typhoid’ ‘ciprofloxacin a kasar nan, ta na mai cewa angano wani kamfanin kasar Indiya da ke saida jabun maganin a kasar nan.

Kamfanin ‘Mars Remedies PVT Limited’ dake hada maganin ba shi da kwarewa sannan yana hada jabun magani ne.

Hukumar ta yi kira da a sa ido matuka domin shan maganin idan ba a sani ba zai iya haddasa wasu cutar.

Shugaban Hukumar Mojisola Adeyeye ta Sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai a Abuja ranar Talata.

Mojisola ta ce jabun maganin ‘ciprofloxacin’ da wannan kamfani ke sarrafawa mai dauke da lamban rajistan hukumar NAFDAC C4-0498 kuma mai nauyin BP 500mg sannan Kamfanin ‘Pinnacle Health Pharmaceutical’ Surulere jihar Legas ne ke dillancin maganin a kasar nan.

A dalilin haka ta ce duk magungunan da Kamfanin ‘Mars Remedies PVT Limited’ ke sarrafawa ta hana shigowa da su kasar nan.

Mojisola ta yi kira ga masu shigo da magunguna da su daina shigowa da wannan maganin a kasar nan.

A watan Afrilun 2020 PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda Hukumar NAFDAC ta gargaddi mutane game da siyan jabun maganin zazzabin cizon sauro wato ‘chloroquine’.

NAFDAC ta bayyana cewa an shigo da su daga kasar Chana ne kuma magungunan duk ba masu kyau bane.

Share.

game da Author