Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga matasan Nijeriya da su yi amfani da damar da aka ba su cikin shirye-shiryen da gwamnatin sa ta fito da su don rage fatara da rashin aikin yi.
Shirye-shiryen, wadanda da Turanci ake kira ‘National Social Investment Programmes (NSIPs)’, ana gudanar da su ne a karkashin Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya domin a kyautata rayuwar matasan da sauran mabukata.
Shugaban ya yi wannan maganar ne a cikin jawabin da ya gabatar ga kasar nan kan tarzomar ‘EndSARS’ a daren Alhamis, 22 ga Oktoba, 2020.
Ya ce duk da raguwar rashin kudin shiga da ƙasar nan ke fama da shi da kuma tarnakin da annobar korona ta kakaba wa kasar, Gwamnatin Tarayya ta fito da tsare-tsare da ke taimaka masu kananan sana’o’i da matasa da fakirai ta yadda za a taimaki rayuwar su.
Ya ce, “Gwamnati ta fito da hanyoyi da tsare-tsare na musamman domin matasa da mata da kuma mutane wadanda ke fama da babu a cikin al’umma. Wadannan sun haɗa da babban shirin mu na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara nan da shekaru 10. Akwai kuma shirin naira biliyan 75 na Asusun Gina Matasa na Kasa inda za a samar da damarmaki ga matasa da kuma kanana da tsaka-tsakin sana’o’i, wato asusun ‘Micro, Small and Medium Enterprises (MSME) Survival Fund’, wanda ta hanyar sa gwamnati ke raba lamunin N30,000 ga kowane daga cikin masu sana’a mutum 100,000 tare da ba su tabbacin sayen kayan da su ka yi.
“Sauran tsare-tsaren sun haɗa da ‘Farmermoni’, ‘Tradermoni’, Marketmoni, da shirin ‘N-Power’ da ya kunshi ‘N-Tech’ da
‘N-Agro’.
“Babu wata gwamnati da aka yi a Nijeriya wadda a tsanake kuma da gaske ta tunkari matsalar fatara kamar yadda mu ka yi.”
Shugaba Buhari ya yi kira ga matasa da su yi la’akari da kuma su dau matakin cin gajiyar waɗannan kyawawan tsare-tsare da wannan gwamnati ta fito da su domin ta kyautata rayuwar su kuma ta hana wasu bata-gari su yi amfani da su domin jawo fitina da nufin wargaza shirin dimokiradiyyar kasar nan.
Ya nanata dagewar gwamnatin sa wajen
inganta rayuwar jama’a da kuma tabbatar da hadin kan kasar nan.
Discussion about this post