An cafke barayin taraktoci 48 cikin 110 da aka sace a jihar Adamawa

0

Gwamnatin ta gano taraktocin ne bayan gwamnan jihar Ahmadu Fintiri ya yi barazanar rusa gidan duk wanda aka kama da kayan da aka sata daga dakin ajiya na gwamnati.

Matasa da magidanta sun saci akalla taraktoci 110 dake dakin ajiyan Kaya na kungiyar ‘North East Commodity Association (NECAS)’ dake Yola.

NECAS kungiyar ce dake aikin inganta aiyukan noma a jihohin dake yankin Arewa maso Gabas.

Shugaban kungiyar Sadiq Umar-Daware ya ce matasa da magidanta sun fasa dakunan ajiyan kaya na kungiyoyin manoman shinkafa da masara inda suka sace buhunan taki, wake, Shinkafa, Masara da sauran kayan abinci.

“An sace buhunan wake, shinkafa, masara, dawa, gero, tsaban Kudi, kujeru, babura, na’urorin komfuta da sauran su daga ofishin su.

Umar-Daware ya yi kira ga mutane da su kai karan duk wanda suka gani da kayan da aka sata na wadannan kungiyoyi a ofishin jami’an tsaron mafi kusa da su.

An rika nuna wasu matasa akan taractocin a Yola suna turawa, wasu kuma ma har mai suka saka musu suka tuka su zuwa inda suke.

Sai dai kuma gwamna fintiri ya ce wa barayin cewa ba zai bari su ci bulus ba. Ko ka dawo da kayan ko kuma isan aka kama ka da su a rusa gidan ku kacokan.

Share.

game da Author