SATAR ABINCI: Rundunar Tsaro na Sibul Difens ta sallami ma’aikacinta da ya shima yayi warwaso a rumbun gwamnati

0

Rundunar tsaro na Sibul Difens (NSCDC) na Abuja ta sallami wani ma’aikacin ta mai suna illiya Ibrahim bayan ta kama shi da laifin satan kayan tallafin korona da gwamnati ke ajiye da su a daya daga cikin rumbun ajiyan Kaya dake Gwagwalada Abuja.

Mataimakin shugaban yada labarai na hukumar Ekunola Gbenga ya sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Talata.

A bayanin da ya yi shugaban hukumar Abdullahi Gana ya ce an kafa kwamiti domin yin da binciken zargin satan kayan ajiyan na gwamnati da aka yi wa Ibrahim.

“Sakamakon bincike da kwamitin ta gabatar ya tabbatar cewa Ibrahim ya saci kayan tallafin korona dake dakin ajiyan kaya na gwamnati a Gwagwalada.

Ibrahim Iliya, jami’in Sibul Difens shima ganin arha ya sa ya manta jami’in tsaro ne, ya biya wa barayin matasa suka rika jidar kayan ajiya a rumbuna gwamnati da suka farfasa.

Gana ya ce bisa ga wannan sakamako hukumar ta sallami Ibrahim daga aiki kwata-kwata.

Ya yi kira ga mutane da su ci gaba da bada bayanan da za su taimaka wajen gano ma’aikatan da bata gari ne a cikin sauran.

Tun a makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES ke bada labarin yadda masu zanga-zangar a rusa rundunar SARS suka rikida zuwa ‘yan ta’adda suna satan kayan abinci da na mutane a dakunan ajiyan na gwamnati da na mutane.

Zuwa yanzu gwamnati ta dauki wasu matakai da suka taimaka wajen kamo barayin da kayan da suka sace sannan da yanke musu hukunci.

Haka kuma a ranar Talata irin wadanna barayin matasa sun afka wa dakin ajiye kaya na hukumar kula da dalibai masu yi wa kasa hidima wato NYSC dake kubwa Abuja.

Barayin matasan sun dira ofishin NYSC ne tun da sanyi safiya, da misalin karfe 8 suna jidan katifu, babura da duk wani abin amfani da suka ci karo da da su a dakin ajiyan.

Share.

game da Author