Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shawarci jam’iyyun siyasa da ƴan takara da jami’an tsaro da su yi aiki tsakanin su da Allah a zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Edo a ranar Asabar ɗin nan.
A cikin sakon da ya aike wa da masu zaɓe da jam’iyyun siyasa da jami’an zabe da na tsaro, shugaban ya kuma yi gargadi kan abin da ya kira “tunanin siyasa irin na ko-a-mutu-ko-ai-rai.”
Mai taimaka wa shugaban kasa kan al’amurran aikin jarida da yada labarai, Malam Garba Shehu, shi ne ya bada takardar shawarar da shugaban ya bayar a Abuja inda ya ruwaito Buhari ya na fadin: “Na yi matukar sadaukar da kai na ga tabbatar da zabe cikin adalci, to amma tawa sadaukarwar ba ta wadatar ba ita kaɗai idan sauran masu ruwa da tsaki da ke wajen zaben ba su bi ka’idoji ba.
”Ina so in ga an ɗaga darajar dimokiradiyya a ƙasar nan a kowane mataki, amma hakan ba zai samu ba idan su ‘yan siyasa sun hau matsayin a-mutu-ko-ai-rai don kawai su samu mulki ko ta halin kaka.
“Tunani irin na a-mutu-ko-ai-rai a siyasa barazana ne ga zabe cikin adalci da kwanciyar hankali domin su ‘yan siyasar sun fi maida hankali ne ga cin zaben maimakon su damu da samuwar sakamako cikin adalci wanda zai nuna bukatar mutane masu zabe.”
Shugaban ya yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su da su bi doka da oda.
Ya shawarci jami’an zabe da na tsaro da “su kasance ‘yan baruwan mu don tabbatar da an yi zabe cikin kwanciyar hankali kuma cikin adalci. kuma su guji aikata duk wani abu da zai iya bata darajar zaɓen.”
Ya ce: ”Gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da adalci ya na daga cikin manyan abubuwan da na tsare a dimokiradiyyar mu, kuma ina so wannan sadaukarwar ta kasance daya daga cikin gadon da zan bar wa ‘yan baya idan na bar mulki.”
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta kammala dukkan shirye-shirye don gudanar da zaben gwamnan Jihar Edo a gobe Asabar.
Haka kuma ya ruwaito cewa ɗan takarar jam’iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu, da na jam’iyyar PDP Godwin Obaseki, wadanda su ne manyan ‘yan takarar da za su gwabza, sun riga sun rattaba hannu a kan wata takardar yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a zaben.