ZABEN EDO: Abubuwa 30 dangane da muhimmancin Jihar Edo a Najeriya

0

1. Jihar ta na cikin bangaren tsohuwar Jihar Bendel, har zuwa 1991.

2. An kirkiro Jihar Edo a ranar 27 Ga Agusta, lokacin da aka ciri Jihar Delta duk a cikin Bendel, 1991.

3. Benin ne babban birnin Jihar Edo, kuma shi ne dai hedikwatar Yankin Midwestern Region cikin 1963. Shi din ne kuma babban birnin Jihar Bendel bayan kirkiro ta a 1976.

4. An kirkiro Jihar Bendel daga tsoffin Gundumomin Benin da Delta.

5. Sunan Gidan Gwamnatin Jihar Edo Denis Osadebay House.

6. Denis shi ne Firimiyan Midwest na farko kuma daga shi ba a sake yin wani ba. Dan asalin garin asaba ne.

7. Jihar Edo na cikin Jihohi shida da su ka kunshi Yankin Kudu maso Kuku.

8. Kididdigar yawan jama’a ta 2006 ta nuna akwaai mutum milyan 4,235,595.

9. Jihar Edo na da Kananan Hukumomi 18 mazabu 193.

10. Edo na da fadin kasa murabba’in kilomita 17,802.

11. Jihar Edo na tsakiyar jihohin Delta, Ondo da Kogi.

12. Akwai masu rajistar zabe a jihar Edo mutum 2,210,534. A cikin su mutum 1,726,738 ne su ka karfi katin zabe.

13. Akwai rumfunan zabe 2,627 a Jihar Edo.

14. Kirarin Jihar Edo shi ne, ‘Heartbeat of the Nation’.

15. Ana magana da yare 17 a Jihar Edo, amma wadanda su ka fi rinjaye su ne Bini, Ishan, Afemai da Ora.

16. Akwai Sanatoci uku a Jihar Edo. Biyu na PDP daya kuma na APC.

17. Shiyyar Sanatan Kudu na da Kananan Hukumomi 7. Na Tsakiya Kananan Hukumomi 5, sai na Arewa Kananan Hukumomi 6.

18. Kabilun da su ka yi kaka-gida a Shiyyar Sanatan Kudu sun hada da Bini, amma akwai burbushin kabilar Ijaw, Itsekiri, Urhobo, Yarabawa da kuma Igbo.

19. Shiyyar Sanatan Tsakiya ya kunshi kabilar Ishan (Esan)

20. Shiyyar Sanatan Arewa akwai Afemai, Era, Akoko da kuma tsirarun Igbira.

21. Akwai Shiyyar Mazabu 9 a Jihar Edo.

22. Gwamna Lucky Igbinedion ne ya yi mulki a Jihar Edo daga 1999 zuwa 2007. Zango biyu kenan. A karkashin PDP ya yi mulki.

23. Gwamna Osunbor ne ya gaje shi daga Mayu 2007 zuwa Nuwamba, 2008. Ya fito daga kabilar Ishan, a Edo ta Tsakiya.

24. An tsige shi, kotu ta maye gurbin sa da Adams Oshiomhole na jam’iyyar AC, inda ya narke ACN, daga nan kuma zuwa APC. Oshiomhole ya yi shekara takwas, daga 2008 zuwa 2016.

25. Godwin Obaseki ya gaji Oshiomhole cikin 2016. Dan kabilar Bini ne daga Edo ta Kudu, a karkashin APC. Amma a yanzu ya na takarar neman zango na biyu a karkashin PDP.

26. Gwamnan Edo na Jamhuriya ta Uku, shi ne John Oyegun ( Janairu 1992 zuwa Nuwamba, 1993). Dan kabilar Beni ne. Ya yi shugabancin APC na Kasa baki daya.

27. Farar hula uku sun yi mulkin tsohuwar Jihar Bendel. Su ne Ambrose Alli, Morbid Anthony da Samuel Ogbemudia.

28. Gwamnonin soja biyar ne su ka yi mulkin Jihar Edo, daga 1991 zuwa 1998.

29. Akwai manyan makarantu biyar a Jihar Edo. Su na da Jami’o’i 3 Ma’karantar Fasaha 2.

30. Fitattu da mashahuran da aka yi a Jihar Edo, sun hada da Mataimakin Janar Babangida, wato Agustus Aikhomu, Mataimakin Abdulsalami Abubakar, wato Mike Aikhibe. An yi Anthony Enahoro, wanda a 1953 a Majalisar Yankin Yamma ya fara kawo kudirin neman ‘yanci daga mulkin mallakar Turawan Ingila.

Akwai Micheal Imodu, jagoran siyasar ‘Imudawa’, Shugaban Cocin Christ Embassy, Chris Oyakhilome, Raymond Dokpesi mai AIT da Raypower, John Momoh mai Channels TV, Dele Giwa na Mujallar Newswtach, Anthony Anenih, Abel Goubadia wanda ya taba shugabancin Hukumar Zabe ta Kasa, Ministoci da sauran manya da mashahurai da dama.

Share.

game da Author