KORONA: Mutum 221 suka kamu ranar Juma’a

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 221 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –59, Abia-46, FCT-22, Gombe-20, Filato-17, Rivers-11, Bauchi-7, Benue-6, Ekiti-6, Imo-6, Kaduna-4, Kwara-4, Ondo-4, Ogun-3, Osun-3, Bayelsa-1, Edo-1 da Kano-1

Yanzu mutum 56,956 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 48,305 sun warke, 1,094 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,557 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,827 FCT –5,526, Oyo – 3,226, Edo –2,611, Delta –1,799, Rivers 2,220, Kano –1,734, Ogun – 1,758, Kaduna –2,326, Katsina -845, Ondo –1,594, Borno –741, Gombe – 799, Bauchi – 689, Ebonyi –1,035, Filato -3,192 , Enugu – 1,234, Abia – 835, Imo – 557, Jigawa – 322, Kwara – 1,013, Bayelsa – 394, Nasarawa – 447, Osun – 810, Sokoto – 161, Niger – 250, Akwa Ibom – 288, Benue – 473, Adamawa – 231, Anambra – 232, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 73, Ekiti – 313, Taraba- 95, Kogi – 5, da Cross Rivers – 85.

Najeriya ta kafa kwamitin magance cutar Korona da magungunan gargajiya

Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya kaddamar da Kwamitin Magance Cutar Korona Da Magungunan Gargajiya, domin gano hanyar rabuwa da cutar ta dabarun amfani da magungunan gargajiya da za a rika harhadawa a nan cikin gida.

Cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha, Abdulganiyu Aminu ya fitar a ranar Litinin, ya ce Minista Onu ya yi gargadin cewa har yanzu annobar Korona na yi wa harkokin lafiya da tattalin arzikin kasar nan babbar barazana.

Dalili kenan ya ce akwai gaggawar bukatar a zabura wajen gano dabaru da fasahar amfani da magungunan gargajiya na nan cikin gida domin a yi wa Korona kwaf-daya.

Kwamitin inji Minista, an kafa shi ne tare da dora masa alhakin tantance ikirari da magungunan da wasu likitoci ko masu harhaɗa magungunan zamani da na gargajiya suka yi cewa sun gano maganin warkas da cutar Korona.

Share.

game da Author