Allah ya sawa Ɗan Adam mantuwa. Shi yasa sau da dama mutane ke tunanin gara jiya da yau ba tare da tunanin yadda jiyan nan take sosai ba.
Akwai wani rubutu mai ban sha’awa da Mallam Mahmud Jega ya yi a shekarar 2010 ana bikin cikar Najeriya shekaru 50 da samun ƴancin kai. Mutane na ta cece-kucen gara da da yanzu sai Mallam Mahmud ya yi wani rubutu ya kwatanta rayuwa a shekarun 1960s da 1970s da yadda aka samu cigaba da abubuwan more rayuwa a 2010. Ya bada misalai da dama, harkokin sufuri, yalwar arziki, sadarwa, da sauransu. Har yau in na tuna ina son na sake karanta wancan rubutu.
Na ga ana maganar wasu na cewa gara lokacin Abacha da wannan lokaci da muke ciki. Idan ba tsabar mantuwa ko kuma rashin sani ba ai ban ga yadda za a ce gara a koma wancan lokaci da yanzu ba. Tabbas ana shan wahala kuma akwai mutane dake fuskantar ƙuncin rayuwa a yanzu, amma ko kusa ba zaka hada da halin ƙuncin da mutane da dama suka shiga a waɗancan shekarun ba.
An yi yunwa sakamakon talauci. Akwai abinci amma babu abin saya. Wannnan ta sa talakawa irinmu kirkiro cimaka (abinci) iri-iri don yaki da yunwa. Ƙanzon shinkafa da garin kwaki sun yi matuƙar daraja, gidaje da dama basa iya dora sanwa sau uku.
Mafi yawan mutane basa iya mallakar takalmin da ba silifa ba (takalmin soso na wanka). Idan kana da takalmin fata (dan gida) guda daya sai dai a tattala shi daga sallah sai taro. Shadda kuwa ba duk yaro ba, daga yadi dan Funtuwa sai ɗan China.
Idan ana maganar rashin tsaro, yawaitar fashi da makami a wancan lokaci ba’a magana! Akwai kwanta-kwanta, akwai masu bin gidaje, har cikin manyan unguwanni.
Kamar kowane lokaci dole akwai waɗanda su a wancan lokacin suka fi jin daɗi (a yanzu ma akwai waɗanda basu taba jin daɗi kamar ƴan shekarun nan ba) amma dai wannan kusan shi ne halin mafi yawan jama’a.