Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 296 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –33, Filato-183, FCT-25, Ogun-16, Oyo-7, Ekiti-6, Kwara-5 Ondo-5, Anambra-3, Imo-3, Nasarawa-3, Rivers-2, Gombe-2, Edo-2 da Akwa Ibom-1
Yanzu mutum 55,456 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 43,334 sun warke, 1,067 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,055 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,422 FCT –5,335, Oyo – 3,201, Edo –2,602, Delta –1,768, Rivers 2,193, Kano –1,728, Ogun – 1,703, Kaduna –2,214 Katsina -819, Ondo –1,566, Borno –741, Gombe – 746, Bauchi – 670, Ebonyi – 1,030, Filato -2,928, Enugu – 1,184, Abia – 816, Imo – 537, Jigawa – 322, Kwara – 987, Bayelsa – 391, Nasarawa – 441, Osun – 802, Sokoto – 159, Niger – 244, Akwa Ibom – 283, Benue – 640, Adamawa – 228, Anambra – 226, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 293, Taraba- 91, Kogi – 5, da Cross Rivers – 83.
Yadda gwamnatin jihar Kaduna ke kashe Naira 400,000 akan majiyyacin korona.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai na ci gaba da shan caccaka daga bakin ƴan Najeriya, bayan da ya bayyana cewa Jihar Kaduna ta riƙa kashe wa kowane mai cutar Korona naira 400,000 kafin ya warke.
El-Rufai ya yi wanann bayanin ne a taron Majalisar Sarakunan Arewa, da ya gudana a Kaduna, kuma ya watsa bayanin na sa a shafin Twitter.
A wurin taron ya ƙara tabbatar da cewa sai fa a ci gaba da hattara, domin har yanzu cutar Korona na nan, ba a rabu da ita ba.
Ya ce cuta ce mai cin kuɗade, domin Jihar sa Kaduna ta riƙa kashe naira 400,000 a kan duk mai cutar Korona mutum daya kafin ya warke.
Wannan bayani bai yi wa ƴan Najeriya daɗi ba, inda nan da nan su ka bi shi a guje har cikin shafin sa na Twitter su na caccaka da ragargazar sa.
Idan ba a manta ba, kwanan baya Kwamishinan Harkokin Lafiya na Jihar Lagos, ya bayyana cewa Lagos ta riƙa kashe har naira milyan 1 a kan Mai cutar Korona da ya kusa kai gargadar mutuwa. Shi ma ɗin dai ya sha caccaka kamar El-Rufai.
Dukkan su biyu ɗin dai sun ɗanɗana ciwon Korona sun san zafin sa.
Ga Kadan Daga Caccakar Da Aka Yi Wa El-Rufai:
“Haba Malam! Ka kashe naira 400,000 a kan majiyyacin Korona ɗaya tal? To idan an kawo maganin cutar kuma nawa za a riƙa sayar da shi kenan”. Inji wani.
“Kada a yi saurin ragargazar El-Rufai tukunna. Mu jira mu ga adadin kuɗaɗen da Gwamnatin Kano za ta ce ta riƙa kashe wa duk majiyyacin cutar Korona.” Wani Hasalalle kenan, wanda ya haɗa bayanin na sa da zolayar Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje.
“Naira 400,000? Ashe dalili kenan jihohi suka riƙa takarar zuzuta yawan waɗanda suka kamu a kowace jiha.” Shi ma wani kenan da adadin yawan kuɗaɗen ya gigita shi.
“Kai jama’a, komai a kasar nan dai ba daidai ya ke tafiya ba. Allah ya saukake!” Shi ma wani kenan da ya kasa cewa komai.
“Me ke ba za ka ji ba a kasar nan. Sai dai a fadi adadin kuɗaɗen, ba a kawo bayanin yadda aka kashe su. Ai ba abin mamaki ba ne, a kasar da aka ce an raba wa dalibai abinci gida-gida a lokacin hutun zaman gida saboda Korona.”
Haka ɗimbin jama’a suka ci gaba da ragargazar El-Rufai, duk da dai ba a rasa daidaikun da suka ce, “Ai Malam ba ya nasa kwai sai da zabuwa”, wato duk kuɗin da zai kashe sai ya bi diddigi tukunna.
Discussion about this post