A ranar Alhamis kotun dake kasuwar nama dake garin Jos jihar Filato ta yanke wa wani matashi maisuna Abba Arando mai shekaru 25 hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyu.
Kotu ta yanke wa Arando wannan hukunci ne bayan an kama shi da kaifin satan karas da aka kiyasta kudinshi har naira 65,000.
Alkalin kotun Lawal Suleiman ya ce ya yanke wa Arando wannan hukunci ne bisa laifuka uku da ya aikata da suka hada da shiga gonar mutum ba da izini ba, sata da kuma yaudara.
Suleiman bayan ya caji Arando Kudin belin Naira 20,000 ya hori shi da ya tuba ya nemi aiki na gari ya rika da zaran ya fito gidan yari.
A zaman da kotun ta yi lauyan da ya shigar da kara Ibrahim Gokwat ya ce wani mai gonan karas Ahmad Mohammed ne ya kawo karan Arando ofishin ‘yan sanda dake Laranto a garin Jos.
Daga nan ne ‘yan sanda suka fantsama neman Arando har aka kamashi.
Bayan haka a karshe kotu ta bada belin shi akan naira 20,000. Sannan ta yi masa khudubar ya yi karatun ta natsu ya nisanta kansa da aikata irin haka daga yanzu.