KORONA: Mutum 197 sun kamu ranar Alhamis, Yanzu mutum 55,829 suka kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 197 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 48, Filato-83, Kaduna-17, FCT-16, Ogun-11, Katsina-7, Imo-4, Edo-3, Nasarawa-3, Rivers-2, Bayelsa-1, Oyo-1 da Osun-1.

Yanzu mutum 55,829 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 43,810 sun warke, 1,075 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 10,944 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,504 FCT –5,391, Oyo – 3,210, Edo –2,606, Delta –1,780, Rivers 2,197, Kano –1,728, Ogun – 1,726, Kaduna –2,231 Katsina -826, Ondo –1,575, Borno –741, Gombe – 746, Bauchi – 671, Ebonyi –1,034, Filato -3,037, Enugu – 1,198, Abia – 816, Imo – 541, Jigawa – 322, Kwara – 989, Bayelsa – 391, Nasarawa – 443, Osun – 804, Sokoto – 159, Niger – 244, Akwa Ibom – 283, Benue – 640, Adamawa – 230, Anambra – 226, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 299, Taraba- 91, Kogi – 5, da Cross Rivers – 83.

Gwamnati zata siyo na’urorin gwajin korona na naira biliyan 8.49

Ganin yadda cutar KORONA ke dada yaduwa a kasar nan gwamnati ta ware naira biliyan 8.49 domin siyo kayan yin gwajin cutar a kasar nan.
A jawabin da ministan kiwon lafiya Osagie Ehinare yayi a wajen taron majalisar zartaswa ta Kasa ranar laraba, ya ce hakan ya zama dole ganin yadda cutar ke dada yaduwa a Najeriya.

Ya ce siyo wadannan na’urori zai taimaka wajen aikin dakile yaduwar annobar Korona a duniya.

Osagie ya ce hukumar NCDC za ta bude sabbin wurare yin gwajin Korona a duk kananan hukumomin dake kasar nan domin dakile yaduwar cutar.

Sakamakon gwajin cutar covid-19 da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba ya nuna an samu karin mutum 453 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.

Share.

game da Author