CBN da Kwamitin Bunkasa Tattalin Arziki sun rukume gardamar rashin tasirin kokarin saukaka kuncin rayuwa lokacin Korona

0

Yanzu dai ta kacame tsakanin Kwamitin Bunkasa Tattalin Arziki da kuma Babban Bankin Najeriya (CBN), inda bangarorin biyu su ke turnukun gardandamin rashin tasiri ko tasirin da shirin saukaka kuncin rayuwar da CBN ya bijiro da shi a lokacin fantsamar cutar Korona a Najeriya.

Yayin da Kwamitin Bunkasa Tattalin Arziki (NESG) ke cewa wasu tsare-tsaren da Gwamnatin Tarayya ta shigo da su a karkashin CBN ba su saukake wa dan Najeriya wani kuncin komai ba, shi kuwa CBN ya kafe kan cewa shirye-shiryen da ya bijiro da su sun ceto tattalin arzikin Najeriya daga tekun masifar da ya nemi nutsewa a ciki.

A ranar Talata ce NSEG suka dauki nauyin buga wani bayani da suka rada wa suna “Batun da ke Bukatar Yin Nazarin Gaggawa,” wanda a ciki suka ragargaji wasu tsare-tsaren da CBN ya aiwatar a fannin noma da kuma tattalin arzikin kasa.

NESG dai kwamiti ne da aka tattaro masana da tattalin arziki da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci da masana’antu aka kafa.

Korafin NESG Ga CBN:

Kwamitin NESG ya ce da yawan tsare-tsaren rage radadin talauci da tayar da komadar tattalin arziki da gwamnati ta bijiro da su saboda Korona, ba su yi wani tasiri ba.

Musamman suka ce wasu tsare-tsaren da CBN ya fito da su, ba su warkar da komai ba. A takaice dai cewa suka yi CBN ya gaza.

Sun ce duk da gwamnati ta gabza kudi a karkashin CBN domin bunkasa noma, shirin Lamunin Noma Ga Kananan Manoma (Anchor Borrowers Programme) bai tsinana komai ba. Bai kawar da yunwa a jiki ko ma a bakin ‘yan Najeriya ba.

Sun kuma yi tir da tsarin da CBN ta yi na musayar kudaden kasashen waje, bada lamunin ramcen gaggawa da kayyade farashin wasu kayayyaki ba tare da tantace wasu ka’idoji ba.

Martanin CBN Ga NESG:

CBN ya ce ko mai hassada ya san cewa tsare-tsaren da ya bijiro da su sun rage kunci da radadin talauci a lokacin Korona. Kuma sun tallafa wa tattalin arziki a matakin sama da tsaka-tsakiya da na kasa wajen hana su durkushewa gaba daya.

Ya kawi tsare-tsaren da ya aiwatar masu yawa, ciki har da daga kafar biyan bashi na tsawon shekara daya cur ga wadanda suka karbi lamuni.

Ya ce Kuma an kirkiro bada lamuni na naira bilyan 59 ga gidaje, kanana da matsakaitan masu sana’o’i

Ya ce an yi wadannan a karkashin NIRSAL Mincrofinace Bank.

“An bada lamunin naira bilyan 100 ga kamfanonin harhada magunguna da sauran masu harkokin hada-hadar sayar da kayan kiwon lafiya, magunguna da sauran su.

CBN ya ce akwai Shirin Bashin Naira Tiriliyan 1 domin bunkasa masana’antun cikin gida.

A haka dai CBN ya rika kawo abubuwan bunkasa tattalin arzikin da ya bijiro da su, wadanda ya ce duk sun yi tasiri.

Share.

game da Author