KORONA: Akalla kamfanoni 300 ne suka amfana da rage kudin yin rajista da NAFDAC ta yi a Kano

0

Akalla kamfanoni 300 ne suka amfana daga rage kudin yin rajistan Kamfanoni da Hukumar kula da Ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC tayi domin kananan masana’antu saboda Korona.

Kodinatan hukumar Shaba Mohammed ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kano ranan Laraba.

Mohammed ya ce hukumar ta rage kashi 80 bisa 100 daga cikin kudin rajistan da kamfanoni ke biya, yanzu Kashi 20 bisa 100 ne kamfanoni ke biya idan za su yi rajistan aiki.

Hukumar ta kuma bai wa kananan masana’antu damar hada man tsaftace hannu ba tare da hukumar ta bincike inganci da sahihancin man ba.

” Hukumar ta yi haka ne saboda ta tabbatar da ingancin kayan da ake amfani da su wajen hada man tsaftace hannu.

” Sannan hukumar ta siya wasu kayan samun kariya daga kamuwa da cutar korona wanda kamfanoni suka sarrafa ta bada su kyauta wa gwamnatin jihar Kano.

Bayan haka hukumar ta hori masu yin buredi da su rika amfani da kayan hada buredi da ake da su a kasar na domin guje wa tsadan abinci a jihar.

Mohammed ya kuma ce tare da hadin guiwar gwamnati, jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki, hukumar ta yi nasaran rage yawan safara da ta’amali da miyagun kwayoyyi a jihar.

Ya ce shekaru biyu da suka gabata hukumar ta kona magungunan da lokacin aikinsu ya kare da ya Kai Naira biliyan 3.2 a jihar.

Share.

game da Author