Hukumar Kula da Basussuka ta Kasa (DMO), ta ce bashin da ake bin Najeriya zuwa watan Maris ya kai naira tiriliyan 31 (wato dala bilyan 85.897).
Ofishin ya ce adadin ya kai naira tiriliyan 31 din ne bayan da aka kara rikito bashin tiriliyan 2.38 na naira, kwatankwacin dala bilyan 6.593 ya zuwa watan Yuni da ya gabata. Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (Debt Management Office) ne ya bayyana haka a ranar Laraba.
DMO ya ce tulin bashin ya kara hawa sama ne daga naira tiriliyan 28.628 zuwa naira tiriliyan 31.009 a watan Maris.
Ofishin DMO ya rarrabe yadda bashin ya rika hauhawa daga wanda aka ciwo a hannun Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), sai kuma wani saura da aka ciwo domin kokarin cike rarar ayyukan da aka gindaya alƙawurran za a yi, a cikin kasafin kudi na 2020.
Sabon bashin da ake bin Najeriya na cikin gida sun hada da: naira bilyan 162.557 daga kuɗin Sukuk da gundarin alƙawarin kidade a rubuce da Najeriya ta bayar, domin a biya masu shigo da kayayyaki daga kasashen ketare.
Bashin Cike Gibin Kasafin Kudi:
Basussukan da ake bin Najeriya wadanda ta ciwo daga waje, sun kai naira tiriliyan 11.363, sai kuma bashin cikin gida na naira tiriliyan 19.945.
Jihohin Najeriya 36 da FCT Abuja ana bin su bashin naira tiriliyan 1.539 duk bashin da suka ciwo daga kasashen ketare. Akwai kuma wani bashin na naira tiriliyan 4.190 da ake bin jihohin wadanda suka ci a nan cikin gida.
Bashin Zai Kara Yawa:
DMO ya ce yawan adadin basussukan zai kara yawa sosai nan da kankanen lokaci. Dalili, saboda akwai bashin da Ba itnkin Duniya da kuma Bankin Musulunci da za su bayar domin a zuba a yi ayyukan kasafin 2020.
Najeriya ta zabtare kasafin kudaden 2020, inda ta rage wasu aykuan da za ta yi, saboda karancin kudaden da annobar cutar korona.
Ofishin DMO ya ce bashin zai karu sosai cikin wannan shekara domin jihohi za su kara kinkimo basussuka masu yawa.
Basussukan Manyan Cibiyoyin Duniya: Yayin da DMO ya yi wa bashin dalla-dalla, kididdiga ta nuna cewa manyan Cibiyoyin Hada-hadar kudade na duniya, su na bin Najeriya nunkin-ba-nunkin bashi. IMF na bin Najeriya bashin dala bilyan 3.359, Bankin Duniya ya bai wa Najeriya lamunin dala bilyan 16.36 shi da Bankin Bunkasa Kasashen Afrika (African Development Bank, ADF).
Wadannan cibiyoyin kudade uku ke bin Najeriya bashin kusan kashi 52% bisa 100% na ilahirin dimbin basussukan da ta ciwo.
Akwai basussukan da Najeriya ta rika rakitowa daga Chana a hannun Exim Bank, har dala bilyan 3.24, sai irin su cibiyoyin kasar Faransa, Japan da sauran cibiyoyi da dama.
Jihohi: Jihar Lagos aka fi bi bashi har naira bilyan 493.32. Sai Rivers naira bilyan 266.94, Akwa Ibom naira bilyan 239.21, sai Delta naira bilyan 235.86.
Wadannan jihohi hudu da aka fi bin su bashi, su ne jihohin da suka fi sauran jihohi karfin arziki.