Mahara sun daka warwason ‘mutum 20’ a Abuja

0

Wasu mahara dauke da manyan bindigogi sun kewaye kauyen Tungar Maje da ke kusa da Zuba, Abuja, inda aka ce sun tsere da akalla mutum 20.

Lamarin ya faru bayan 12:15 tsakar daren Alhamis, bayan sun yi musayar wuta na tsawon lokaci da ‘yan bijilante, inda bayan sun fi karfin su ne suka arce da mutane da dama.

Duk da dai babu takamaimen adadin mutanen da aka yi garkuwar da su, wani mazaunin garin da ya ce a boye sunansa, ya ce wayewar safiyar Alhamis ‘yan bijilante sun shaida musu cewa maharan sun gudu da mutum zai kai 29.

Kakakin Yada Labarai na ‘Yan Sandan FCT Abuja, Anjuguri Mamzah, ya ce ya na nan ya na rubuta bayanin da zai sanar wa manema labarai, dangane da harin.

Shi din ma bai bayyana adadin mutanen da aka yi warkuwar da su ba.

Mazauna Tungar Maje sun ce an kwashe sama da awa daya ana harbe-harbe a kauyen.

Bayan da suka ci karfin ‘yan bijilante da ke garin ne suka sace mutum 20 suka arce da su.

Harin ya faru ne mako daya bayan bayyanar wata wasika daga Hedikwatar Rundunar Kwastan ta Kasa da ke Abuja cewa akwai Boko Haram dankam da suka yi wa Babban Birnin Tarayya, Abuja kawanya.

Rahoton ya ce ‘yan ta’addar sun kafa sansanoni a dazukan Jihar Nasarawa, Neja Kogi da FCT Abuja.

Share.

game da Author