BOKO HARAM: Iyalan sojojin da Boko Haram suka kashe sun kokan kan watsin da aka yi da su

0

Iyalan wasu sojojin da Boko Haram suka kashe a wurin gumurzun yaƙi, sun koka da rashin cika masu alƙawarin biyan su kuɗaɗen giraruti da Hukumar Sojojin Najeriya ta ce za ta biya su da gaggawa. Sun ce har yanzu shiru ka ke ji an watsar da batun su.

Binciken da PREMIUM TIMES ta yi ne ya tabbatar da haka.

Tun a cikin watan Afrilu PREMIUM TIMES ta budanar da wani bincike kan yadda Hukumar Sojoji ta yi watsi da iyalan marigayi Sunday Orji, wani soja mai lamba: 04/55)1725, wanda ya mutu a filin dagar gwabza ƙazamin yaƙi da Boko Haram, a cikin 2015.

Irin watsin da aka yi wa iyalan Sunday Orji bayan Boko Haram sun kashe shi, irin da a yanzu kuma aka yi wa iyalan wani sojan wanda shi ma an kashe shi a filin daga, mai suna Sunday Samuel.

Samuel shi ke da lamba 01/NA/59/725. An kashe shi a wani hari da Boko Haram suka kai a Maiduguri cikin 2017.

Rayuwar Wasu Matan Sojojin Da Boko Haram Suka Kashe Wa Mazaje:

PREMIUM TIMES ta binciko cewa da yawan matan da Boko Haram suka kashe wa mazaje sojoji, a yanzu sun koma sana’ar sarrafa garin kwaki, wanda suke yi daga rogo. Su kuma kananan ‘ya’ysn su ma’karantar ma tuni ta gagare su, an kore su.

Bayan wannan jarida ta buga rahoton rayuwar da Emelia Orji, matar Sunday Orji ta ke ciki, sai Hedikwatar Tsaro ta Sojoji suka tuntube ta a ranar 24 Ga Afrilu. Kuma suka yi mata alkawarin biyan ta hakƙoƙin giratutin mijin ta, sojan da Boko Haram suka kashe. Sun ce a cikin watan Afrilu din za su biya ta, duk kuwa da cewa sun kira ta ne kwanaki shida kafin watan ya kare.

“Sojojin Najeriya sun kira ni daga Abuja bayan sun karanta halin da na ke ciki a cikin jarida. Suka Yi min alkawarin cewa a cikin watan na Afrilu za su biya ni.” Haka ta shaida wa PREMIUM TIMES a cikin Mayu.

Ta ce ta kai dukkan takardun shaidar da suka wajaba a biya ta hakkin mamacin mijin na ta, a Bonny Camp. Amma aka shafe watanni biyar ko magana ba a yi ba.

“Na koma cikin Agusta domin na bibiyi halin da ake ciki, amma shiga ciki ma hana ni suka yi. Sun bar ni da iyali yunwa na ta rarakar mu.” Haka ta shaida wa PREMIUM TIMES a ranar Alhamis.

Haka aka yi wa Janet ‘yar marigayi Sunday Samuel.

Ta shaida wa wakilin mu cewa mako daya bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin ta, sai wasu manyan jami’an sojoji daga Barijin Odogbo a Ibadan suka kai mata ziyara har gida. Sun sanar da ita cewa za a biya ta dukkan hakkin mamacin mijin ta, ba da dadewa ba.

Amma tun daga lokacin har yau, babu abin da aka yi mata.

Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya sun sha bibiyar PREMIUM TIMES su na karbar lamba da adireshin iyalan sojojin wadanda Boko Haram suka kashe wa mazaje, amma ba a yin wani hobbasan biyan su hakkokin mazajen su da aka kashe a fagen yaki da Boko Haram.

Ranar 9 Ga Mayu, Hedikwatar Tsaro ta Sojoji ta shaida wa wakilin mu cewa ta na kan aikin harhada bayanan da nan gaba kadan da zarar an kammala za a biya su giratutin.

Cikin Yuni, wani Major Ohaeri ya nemi lambobin iyalan, tare da cewa sun kusa biyan su. PREMIUM TIMES ta gano cewa ko sau daya bai kira kowa daga cikin iyalan mamatan sojojin ba.

Tun daga lokacin, Kakakin Yada Labarai na Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya, Manjo Janar John Enenche ya ki ya amsa kiran lambar sa da PREMIUM TIMES ta rika yi.

Shi ma Kakakin Yada Labarai na Rundunar Sojojin Najeriya baki daya, Sagir Musa, ya ki ya yi magana a kan lamarin.

Sai dai wasu manyan jami’an sojoji da suka roki PREMIUM TIMES ta sakaya sunayen su, sun ce idan ba a ci gaba da matsa lamba ba, to ba za a biya iyalan mamatan sojojin hakkokin su ba.

Share.

game da Author