GOMBE: Yadda magidanci ya kashe dan matarsa saboda tsananin kishi

0

Jami’an tsaro na ‘Civil Defence’ (NSCDC) a jihar Gombe ta kama wani magidanci, Usman Sama’ila mai shekaru 40 da laifin kashe ɗan matarsa saboda kishi, wato ɗan tsohon mijinta.

Sama’ila mazaunin kauyen Tsakuwama dake karamar hukumar Miga jihar Gombe ya auri mahaifiyar wannan yaro da ya kashe ne bayan aurenta ya mutu da mahaifin wannan yaro mai wata 17.

Kakakin rundunar NSCDC Adamu Shehu wanda ya tabbatar da haka ya ce mahaifiyar yaron ne ta kai karan mutuwar danta a ofishinsu kuma wai tana zargin mijinta ne ya kashe yaron.

Shehu ya ce mahaifiyar yaron mai suna Bahayura ta ce tun bayan auren su Sama’ila ya fara nuna baya son danta.

“Bahayura ta ce sau biyu Sama’ila na yunkurin kashe danta amma Allah baya bashi sa’a sai a wannan karo.

Shehu ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa Sama’ila ya fita da wannan yaro domin ya raka shi gona inda a gonan ne ya shake yaron har ya mutu.

Ya ce Sama’ila ya fada wa matarsa kuma mahaifiyar yaron cewa cutar nimoniya ne ya kashe yaron.

Shehu ya ce a binciken da suka gudanar Sama’ila ya ce ya aikata haka ne domin karkato da hankalin matarsa zuwa gareshi.

Ya ce a ido Sama’ila na kama da wanda ke da hankali amma hukumar za ta aika da shi asibitin mahaukata domin a tabbatar da ko dai wani abu ya taba ƙwaƙwalwar sa.

Bayan haka ne za a gurfanar da shi a kotu.

Share.

game da Author