Hukumar Zabe ta Kasa ta bayyana cewa za a ji matsayar ta dangane da soke zaben gwamnan Bayelsa da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta yi, a lokacin duk da kotu ta damka mata kwafe-kwafen bayanan hukuncin wanda ta yanke.
Kwamishinan Zabe na Kasa kuma Jami’in Wayar da Kan Jama’a a kan Zabe, Festus Okoye ne ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a ranar Litinin a Abuja.
Hukumar zaben na magana ne a kan soke zaben gwamnan Bayelsa da kotu ta yi a ranar Litinin, zaben da Gwamna Duoye Diri ne ya lashe.
Amma kuma Okoye ya ce jam’iyyar ANDP bai halasta ta shiga zaben ba, saboda ba ta shigar da kara cikin wa’adin kwanaki 14 da dokar zabe ta kasa ta gindaya ba.
Okoye ya tunatar cewa ANDP ta shigar da batun neman tsayawa takara ne a ranar 16 Ga Nuwamba, 2019 na zaben Gwamnan Bayelsa.
Daga nan ya kara da cewa jam’iyyar ta je ta yi zaben fidda-gwani inda ta mika wa INEC sunan Peter David matsayin dan takarar su na zaben gwamnan Bayelsa.
“Ya zuwa lokacin da aka mika sunan dan takarar ANDP, ya na da shekaru 34 ne, maimakon mafi karancin shekarun takarar dan takarar gwamna shekaru 35 ne, kamar yadda Sashen Doka na 177(b).
“Takardun haihuwar dan takarar sun nuna cewa an haife shi a ranar 10 Ga Fabrairu, 1985.
Okoye ya ce sai da INEC ta turo wa Ofishin ANDP wasikar rashin cancantar dan takari su, Kuma suka amince har suka maye gurbin sa da sunan wani Inowei Janeth a matsayin dan takarar mataimakin gwamna.
Mai Shari’a Ibrahim Sirajo ne ya jagoranci sauran alkalan da suka yanke hukuncin cewa zaben gwamnan Bayelsa haramtacce ne, saboda an cire sunan ANDP a zaben
Ta ce ANDP na da hujjar garzayawa kotu saboda an cire ta daga zaben,wanda kotun ta ce a sake wani zaben cikin kwanaki 90.